An Cafke Jigon NNPP kan Zargin Sukar Gwamna Zulum, Ana Fargabar Kai Shi Kotu
- Rundunar ‘yan sanda a Borno ta kama jigon NNPP, Attom Magira kan zargin sukar gwamna Babagana Umara Zulum
- Rahotanni sun ce an tsare Magira ne saboda tallar hadakar jam’iyyun adawa da magoya bayansa suka sanya a jihar
- An tabbatar da cewa har yanzu yana tsare, amma babu tabbacin ko za a gurfanar da shi a kotu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Borno - Rundunar ‘yan sanda a jihar Borno ta kama wani jigon jam’iyyar NNPP, Attom Magira.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa an kama Magira ne kan sukar da ake zarginsa da yi wa gwamna Babagana Zulum.
An cafke jigon NNPP a jihar Borno
Hadimin jigon NNPP, Mohammed Yahaya ya tabbatar da cewa an kama shi a ranar Lahadi 22 ga watan Disambar 2024, kamar yadda aka wallafa a shafin Facebook na dan siyasar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Attom Magira ya yi takarar gwamna a jam’iyyar APC a shekarar 2019 wanda ya kasance fitaccen mai sukar gwamnatin jihar.
Rahotanni sun nuna cewa an kama shi ne saboda wani allo mai da ke dauke da rubutun neman shirin hadakar jam'iyyun adawa.
Allon na dauke da rubutun ne domin hadin kan tsakanin jam’iyyun siyasa a jihar saboda kawo karshen APC.
Ana zargin gwamnatin Borno da take yan adawa
An tabbatar da cewa wasu bata-gari sun lalata allon da ke dauke da hoton Mariga da ake zargin gwamnatin jihar a kokarin hana kowane irin adawa a jihar.
"Wata majiya ta ce tun 1999 gwamnatin na fatattakar masu adawa, amma Magira bai daina yin adawa mai karfi a jihar ba."
"Magira na tsare tun ranar Litinin 23 ga watan Disambar 2024 amma babu tabbacin ko za a kai shi kotu."
- Mohammed Yahaya
Kokarin jin ta bakin kakakin rundunar yan sanda a jihar, ASP Nahum Kenneth Daso ya ci tura.
An kama mawakin jam'iyyar APC a Kano
Kun ji cewa ana zargin yan Kwankwasiyya da hannu a kama wani mawakin siyasa a Kano mai suna Idris Danzaki a jihar.
Rahotannin sun tabbatar da cewa an kama mawakin ne a ranar 18 ga watan Disambar 2024 a cikin ofishinsa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng