Ganduje Ya Tarwatsa Shirin NNPP, Dan Takarar Gwamna Zai Sauya Sheka zuwa APC

Ganduje Ya Tarwatsa Shirin NNPP, Dan Takarar Gwamna Zai Sauya Sheka zuwa APC

  • Injiniya Popoola Olukayode Joshua na shirin barin NNPP zuwa APC don taimakawa jam'iyyar ta kwace mulkin Oyo a 2027
  • Injiniya Popoola shi ne dan takarar NNPP a zaben Oyo na 2023 kuma an ce ya gana da Ganduje a Abuja a shirin sauya sheka
  • Rahoto ya nuna cewa Abdullahi Ganduje ya bukaci a fara shiri na wuri-wuri domin tazarcen Bola Tinubu da nasarar APC a Oyo

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Oyo - Ana sa ran Injiniya Popoola Olukayode Joshua (POJ), tsohon dan takarar gwamna na NNPP a Jihar Oyo, zai koma jam’iyyar APC ba da dadewa ba.

POJ, tsohon shugaban ayyukan gine-gine na tarayya a Legas, ya bar PDP zuwa NNPP a 2022 don ya kayar da Gwamna Seyi Makinde a 2023.

Majiyoyi sun yi magana kan shirin dan takarar gwamnan NNPP na komawa APC
Akwai yiwuwar dan takarar NNPP a jihar Oyo ya sauya sheka zuwa APC nan ba da jimawa ba. Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Dan takarar NNPP na shirin komawa APC

Kara karanta wannan

NNPP ta zargi Ganduje da hannu a farautar babban jami'in gwamnatin Kano

APC tana shirin karbe mulki daga PDP a 2027, inda ake hasashen POJ zai yi aiki tare da APC don cimma wannan buri a cewar rahoton The Guarian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A makon nan, Injiniya Popoola ya tabbatar da jita-jitar ta hanyar halartar wani taro a fadar shugaban kasa, inda ya gana da Ganduje.

Wasu abokan aikinsa sun tabbatar da wannan lamari, inda suka ce shugaban APC na Oyo, Alhaji Moshood Abas, yana jiran POJ ya shiga jam’iyyar.

Ganduje ya fadi shirin APC na 2027

Shugaban APC na kasa, Ganduje, ya bukaci ‘yan jam’iyyar da su mai da hankali wajen tabbatar da tazarcen Shugaba Bola Tinubu a 2027.

Ganduje ya yi wannan bayani ne yayin wani taro tare da shugabannin APC na Oyo a Abuja, inda ya jaddada bukatar kwato mulkin jihar.

Ya bukaci a fara shiri tun wuri da kuma nemowa jam'iyyar mutane daga gundumomi domin tabbatar da nasarar APC a Oyo da tazarcen Tinubu.

Kara karanta wannan

'Ka yi amfani da basirarka': Ministan Tinubu ta roki Ganduje a kwace mulkin PDP

Gwamnan Oyo ya yiwa Ganduje martani

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnan Oyo, Seyi Makinde ya gargadi shugaban APC na kasa Abdullahi Umar Ganduje kan ikirarin kwace jihar a 2027.

Makinde ya bukaci Ganduje da ya farka daga barcin da yake yi yana mai cewa jam'iyyar APC ba za ta iya kwace jihar Oyo da Osun a babban zaben kasar mai zuwa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.