"PDP Ta Mutu Murus," 'Yar Majalisar Tarayya Ta Ɗauki Zafi bayan Ta Koma APC
- Ɗiyar tsohon gwamnan jihar Delta da ke Majalisar wakilai, Erhiatake Ibori-Suenu ta ce PDP ta mutu murus kuma za su ƙarasa ɓirne ta
- Ƴar Majalisar mai wakiltar mazaɓar Ethiope ta yi wannan furucin ne a wurin taron rabon kayan tallafi ga masu kananan sana'o'i
- A wurin taron, wasu ƙarin ƴan jam'iyyar PDP sun sauya sheƙa zuwa APC, lamarin ya jefa ƴan jam'iyyar a Delta cikin farin ciki
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Bayelsa - Ƴar majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Ethiope a jihar Delta, Hon. Erhiatake Ibori-Suenu ta bayyana cewa jam'iyyar PDP ta mutu a mazaɓarta.
Ibori-Suenu, ɗiyar tsohon gwamnan Delta, James Ibori ta faɗi haka ne a wurin taron raba kayan tallafi ga al'ummar mazaɓarta.
Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, ƴar Majalisar ta rabawa mutanen mazaɓarta motoci, babura, keken dinki da famfunan feshi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yar Majalisa ta caccaki PDP a jihar Delta
Da take jawabi a wajen taron, Ibori-Suenu ta ce dama tun farko zuciyarta na tare da APC a siyasance duk da kasancewarta ‘yar PDP a baya.
Ta bayyana farin cikinta da komawa APC a hukumance, inda ta ce babu kamar jam'iyya mai mulki.
"Guguwa da walƙiya da za su ruguza PDP gaba ɗaya sun iso, za mu birne PDP a kogin Ologbo wanda ke tsakanin jihohin Delta da Edo," in ji ta.
Ɗiyar Ibori ta zargi PDP da tauye haƙƙi
‘Yar majalisar ta zargi jam’iyyar PDP da tauye mata burinta na siyasa, inda ta ce dama tuntuni ta yanke shawarar haɗewa da APC.
Ta gode wa shugabannin APC bisa goyon bayan da suka ba ta, ta kuma yi alkawarin yin aiki tukuru don ganin jam’iyyar ta cimma muradunta a mazabar Ethiope.
Ƙarin ƴan jam'iyyar PDP sun sauya sheka zuwa APC a wurin taron, lamarin ya ajefa mambobin APC cikin farin ciki da murna, rahoton Guardian.
Hadimin Tinubu ya roki jigo ya dawo APC
Rahoto ya gabata cewa hadimin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya fara zawarci da rokon tsohon ɗan takarar gwamnan Bayelsa ya dawo APC.
Tokoni Peter Igoin, mai ba Tinubu shawara kan harkokin fasahar zamani ya buƙaci ɗan siyasar ya dawo APC su haɗu su marawa shugaban ƙasa baya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng