Shugaban PDP na Fuskantar Matsala daga Arewa, Za a Raba Shi da Kujerarsa

Shugaban PDP na Fuskantar Matsala daga Arewa, Za a Raba Shi da Kujerarsa

  • Shugabannin PDP sun yanke shawarar nada dan Arewa ta Tsakiya a matsayin wanda zai maye gurbin Umar Damagum
  • Jagororin yankin sun ce kundin tsarin PDP ya tanadi cike guraben mukamai daga yanki daya idan babu wanda ke rike da su
  • Shugabannin sun kuma fadawa 'ya'yan jam'iyyar abin da ya kamata su yi domin dawo da martabar PDP a idon duniya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kusoshin jam’iyyar PDP a Arewa sun ce za su gabatar da wanda zai maye gurbin shugaban riko na kasa, Umar Damagum, a farkon shekara mai zuwa.

Hakan na kunshe a wata sanarwar bayan taro da aka yi a Abuja tare da tsofaffin shugabannin majalisar dattawa biyu, tsofaffin gwamnoni hudu da sauran shugabanni.

Kusoshin PDP a Arewa ta Tssakiya sun yi magana kan karbe kujerar shugaban riko na kasa
Ana kokarin nada dan Arewa ta tsakiya a matsayin shugaban PDP na kasa. Hoto: @OfficialPDPNig
Asali: Facebook

Za a raba Damagum da shugabancin PDP?

Kara karanta wannan

"Akwai lauje cikin nadi," Atiku ya zargi gwamnati da siyasantar da alkaluman NBS

Kusoshin PDP sun ce ana tuntubar shugabannin jam’iyyar domin karbe kujerar daga hannun Damagum tare da nada wani daga Arewa ta Tsakiya, inji rahoton The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce:

"Shugabannin PDP sun duba halin da jam’iyyar ke ciki, musamman kujerar shugaba na kasa da ta zama babu mai rike da ita.
"Kundin tsarin PDP ya tanadi cewa idan wata kujera ta zama babu mai rike da ita, za a maye gurbinta daga yanki daya bisa sashe na 47 (6)."

Sun ce dole ne shugabannin PDP su ajiye bambance bambancensu domin dawo da hadin kai a jam’iyya ta hanyar yin sulhu da jajircewa.

An roki shugabannin jam'iyyar PDP su hada kai

Shugabannin Arewa ta Tsakiya sun roki sauran shugabannin Arewa da su maido da kujerar shugaban jam’iyyar zuwa yankin domin kammala wa’adin mulkinsu.

Sun bayyana cewa dole shugabannin yankin su yi aiki tare domin samun goyon bayan sauran yankunan Arewa.

Kara karanta wannan

Gwamna da wasu ƙusoshi sun sake taso da Batun Tsige Shugaban PDP na ƙasa

"Babu wata baraka a Yankin Arewa ta Tsakiya, kuma za a ci gaba da kare martabar PDP a matsayin hanyar samar da shugabanci nagari a Najeriya."

- A cewar sanarwar.

Manyan 'yan siyasa sun hadu a taron PDP

Taron ya samu halartar shugabannin PDP irinsu Caleb Muftwang, David Mark, Bukola Saraki, Abba Moro, Jonah Jang, da sauran shugabanni da sanatoci.

Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da Labaran Maku, Jerry Gana, Isa Dobi, Dino Melaye, Margaret Icheen, tare da tsoffin ministoci da gwamnoni.

Gwamnoni 6 na goyon bayan tsige Damagum

A wani labarin, mun ruwaito cewa an samu baraka a tsakanin kungiyar gwanmonin PDP kan batun tsige Umar Damagum daga shugaban jam'iyyar na kasa.

A halin yanzu, wasu gwamnonin PDP shida sun fara matsin lamba a kan a sauke Damagum daga kujerar shugaban riko na kasa tare da nada wani daban.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.