NNPP Ta Zargi Ganduje da Hannu a Farautar Babban Jami'in Gwamnatin Kano

NNPP Ta Zargi Ganduje da Hannu a Farautar Babban Jami'in Gwamnatin Kano

  • Jam'iyyar adawa ta NNPP ta zargi shugaban APC na kasa da biye wa ciyar mulki wajen amfani da jami'an tsaro
  • Jami'in hulda da jama'a na NNPP, Johnson Ladipo ya ce an jibge 'yan sanda don kama jami'in gwamnatin Kano
  • Ya yi zargin cewa an aiko 'yan sanda daga Abuja domin su cafke Sanusi Bature Dawakin Tofa bisa umarnin Sufeto Janar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Jam'iyyar NNPP da ke mulki a Kano ta yi zargin APC da yin amfani da karfin ikon gwamantin tarayya wajen muzguna wa 'yan adawa.

Jam'iyyar ta ce akwai tsoro a cikin yadda ake zargin shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje da hannu a farautar darakta janar na yada labaran gwamna Abba Kabir Yusuf.

Kara karanta wannan

"Akwai lauje cikin nadi," Atiku ya zargi gwamnati da siyasantar da alkaluman NBS

Ganduje
NNPP ta zargi Ganduje da barazana ga jami'in gwamnatin NNPP Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje/Sanusi Bature D-Tofa
Asali: Facebook

Jaridar The Guardian ta wallafa cewa wannan na kunshe a cikin sanarwar da jami'in hulda da jama'a na NNPP na kasa, Ladipo Johnson.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana zargin APC da amfani da 'yan sanda

Jaridar Punch ta wallafa cewa NNPP ta fara zargin APC da yik amfani da 'yan sanda wajen cin zarafi da barazana ga Sanusi Bature Dawakin Tofa.

Jami'in hulda da jama'a na NNPP na kasa, Ladipo Johnson ya bayyana cewa ana zargin 'yan sanda da barazana har ga wasu daga cikin iyalan hadimin gwamnan.

An zargi 'yan sanda da fatali da doka

Jam'iyyar hamayya ta NNPP ta zargi rundunar'yan sandan kasar nan da jam'iyyar APC da kokarin kama Sanusi Bature duk da umarnin kotu da ya haramta hakan.

Jam'iyyar ta roki Sufeto Janar na 'yan sandan kasa, Kayode Egbetokun da ya sa baki a cikin lamarin domin hana amfani da su wajen cimma wata manufa ta siyasa.

Kara karanta wannan

An cafke fitaccen mawakin siyasa a Kano, an zargi yan Kwankwasiyya da hannu

Hadimin gwamna na wasan buya da 'yan sanda

A wani labarin, mun ruwaito cewa darakta janar a kan yada labaran gwamnatin Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya bayyana halin da jami'an 'yan sanda suka jefa shi.

Sanusi Bature ya bayyana cewa jami'an rundunar 'yan sandan kasar nan su na nemansa ruwa a jallo bayan karbar korafin da shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje ya shigar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.