'Ba Ka da Iko': Gwamnatin Tinubu Ta Soki Gwamnan APC da Majalisa kan Taba Ciyamomi
- Gwamnatin Tarayya ta kalubalanci Majalisar dokokin jihar Edo kan dakatar da shugabannin kananan hukumomi
- Ministan shari'a, Lateef Fagbemi shi ya yi wannan martani inda ya yi Allah wadai da matakin da Majalisar ta dauka a jihar
- Hakan ya biyo bayan dakatar da shugabannin kananan hukumomi 18 da mataimakansu da Majalisar ta yi a ranar Talata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Gwamnatin Bola Tinubu ta yi fatali da matakin Majalisar jihar Edo kan shugabannin ƙananan hukumomi guda 18 da mataimakansu.
Gwamnatin ta bakin Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi (SAN) ya yi Allah wadai da dakatarwar da Majalisar Edo ta yi wa shugabannin kananan hukumomi.
Majalisar Edo ta dakatar da shugabannin kananan hukumomi
Fagbemi ya ce duk da cewa ba a kai ga samun cikakken bayani kan lamarin ba, an saba doka kan lamarin, cewar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan ya biyo bayan dakatar da shugabannin kananan hukumomi guda 18 tare da mataimakansu na tsawon watanni biyu.
An ruwaito cewa 'yan majalisar jihar sun dauki wannan matakin ne bayan wani korafi daga gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo.
Okpebholo ya zargi shugabannin kananan hukumomin da nuna rashin biyayya ga umarninsa na mika bayanan kudadensu zuwa gare shi.
Ciyamomi: Gwamnatin Tinubu ta soki Majalisar Edo
Ministan shari'a, Fagbemi ya ce dokar Najeriya ba ta bai wa Majalisar ikon dakatar da shugabannin kananan hukumomi da aka zaba ba.
Ya bayyana cewa, hukumar da ke da ikon daukar irin wannan mataki ita ce Majalisar Dokokin Kananan Hukumomi kadai.
“Abu ɗaya da na sani kuma zan iya faɗi ba tare da tsoro ba shi ne, ƙarƙashin wannan mulki na yanzu, gwamna ba shi da damar tsige kowanne shugaban ƙaramar hukuma.”
- Lateef Fagbemi
Wannan hukunci ya takaita gwamnonin jihohi daga tsoma baki cikin harkokin shugabannin ƙananan hukumomi da aka zaɓa, Punch ta ruwaito.
Ciyamomi sun kalubalanci gwamna kan dakatar da su
Kun ji cewa kwana daya bayan Majalisar jihar Edo ta dakatar da shugabannin kananan hukumomi, sun kalubalanci gwamna.
Shugabannin kananan hukumomi 18 da ke jihar sun yi Allah wadai da matakin da Majalisar da dauka inda suka ce an saba dokar kasa
Wannan na zuwa ne bayan Majalisar ta dakatar da su da mataimakansu a ranar Talata 17 ga watan Disambar 2024 da muke ciki.
Asali: Legit.ng