An Cafke Fitaccen Mawakin Siyasa a Kano, an Zargi Yan Kwankwasiyya da Hannu

An Cafke Fitaccen Mawakin Siyasa a Kano, an Zargi Yan Kwankwasiyya da Hannu

  • Ana zargin yan Kwankwasiyya da hannu a kama wani mawakin siyasa a Kano mai suna Idris Danzaki a jihar
  • Rahotannin sun tabbatar da cewa an kama mawakin ne a jiya 18 ga watan Disambar 2024 a cikin ofishinsa
  • Ana zargin hakan bai rasa nasaba da wata waka da ya yi da ake ganin ya yi cin mutunci ga Sanata Rabiu Kwankwaso

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Jam'ian tsaro sun kama fitaccen mawakin siyasa, Idris Danzaki yayin da yake cikin ofishinsa.

An kama mawakin ne a daren jiya Laraba 18 ga watan Disambar 2024 duk da ba a bayyana dalilin cafke shi ba.

An kama mawakin siyasa a Kano da ake zargin akwai hannun yan Kwankwasiyya
Jami'an tsaro sun cafke mawakin siyasa a Kano. Hoto: Idris Danzaki.
Asali: Facebook

Jami'an tsaro sun kama mawakin siyasa

Hakan ya kunshe ne a cikin wata sanarwa da shafin mawakin ya yada a jiya Laraba a manhajar Facebook.

Kara karanta wannan

Mutane da dama sun rasu da taron murna ya turmutse a makarantar Musulunci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duk da ba a bayyana dalilin cafke mawakin ba amma ana zargin jami'an tsaron sun zo ne da rakiyar yan Kwankwasiyya.

Mawakin ya yi wakoki da dama ga Sanata Kawu Sumaila da ke wakilar mazabar Kano ta Kudu da Hon. Alhassan Ado Doguwa.

Yadda aka kama mawakin a ofishinsa

Sanarwar ta ce ana zargin masu jajayen huluna da hannu a lamarin inda ta bukaci taimakon al'umma da addu'o'i.

A cikin sanarwar, an tabbatar da cewa jami'an tsaron sun shiga har cikin ofishin mawakin kafin cafke shi.

"Innalillahi wainna Ilaihir Rajiun, yanzu jami'an tsaro sun zo har ofis suka kama mawaki, Idris Danzaki."
"An kama shi ne tare da rakiyar wasu masu jar hula, muna neman addu'arku Allah ya fito da shi lafiya, Ameen."

- Cewar sanarwar

Rarara ya fara gina masallacin Juma'a

Kun ji cewa mawakin siyasa, Dauda Rarara ya kai ziyara garin Kahutu da ke jihar Katsina, inda ya duba aikin masallacin Juma'ah da yake ginawa.

Kara karanta wannan

Kwana 1 ga barazanar Turji, an yi kazamar fada tsakanin yan bindiga, an rasa rayuka

A yayin ziyarar, Rarara ya ziyarci sabon gidan biredinsa mai suna Mama Bread, tare da abokinsa Abdullahi Alhikima.

An yada hotunan Rarara da Alhikima suna cin biredi cikin nishadi a gidan biredin da ya bude a karamar hukumar Danja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.