'Ka Yi Amfani da Basirarka': Ministan Tinubu Ya Roki Ganduje kan Kwace Mulkin PDP
- Minista a Najeriya ya yi magana kan zaben jihar Oyo inda ya roki shugaban APC, Abdullahi Umar Ganduje
- Ministan makamashi, Adebayo Adelabu ya bukaci Ganduje ya yi amfani da basirarsa wurin kwace mulkin PDP a Oyo
- Adelabu ya ce a yanzu jam'iyyar APC a Oyo ta hada kai fiye da a baya domin shirin karbe mulki daga PDP
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Oyo - Ministan Makamashi, Adebayo Adelabu ya bukaci shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya kwace jihar Oyo.
Ministan ya roƙi Ganduje da ya yi amfani da nasarorin da ya samu a jihohin Edo da Ondo domin kwato jihar daga Gwamna Seyi Makinde.
Minista ya roki Ganduje kan zaben Oyo
Adelabu ya yi wannan roƙo ne lokacin da ya jagoranci tawagar shugabannin APC na jihar Oyo da 'yan Majalisar Dokoki a Abuja, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ministan ya tabbatarwa shugabancin jam’iyyar cewa APC a Oyo ta koyi darasi kan halin da ta shiga .
Ya ce jam'iyyar ta kuma samu haɗin kai tsakanin dukkan ɓangarori da shugabannin da suke jin haushin juna a jihar, Tribune ta ruwaito.
“Muna so ka taimaka mana ka yi wa shugaban jam’iyyarmu a jihar jagora tare da ba shi goyon baya domin ya cim ma nasarorin da ka nuna a matakin ƙasa."
"Ina da tabbacin zai koyi darasi, muna farin ciki da cewa a karon farko bayan zaɓe na baya, APC a Oyo tana magana da murya ɗaya."
- Adebayo Adelabu
Minista ya ba da tabbacin nasara a zabe
Ministan ya ce yana da tabbacin sun rasa zaɓuɓɓukan baya guda biyu ba saboda rashin farin jinin jam’iyyar a jihar ba sai dai saboda rarrabuwar kai.
“A shekarar 2019, lokacin da nake ɗan takarar gwamna, mun samu rarrabuwar kai, ba mu iya yin sulhu kafin zaɓe ba."
"Mun samu sanatoci biyu da kuma kusan ‘yan majalisar wakilai 10, saboda haka kun san cewa APC a jihar Oyo jam’iyyar jama’a ce.”
- Adebayo Adelabu
Ganduje ya sha alwashin karbe mulkin Rivers
A baya, kun ji cewa Shugaban jam'iyyar APC, Dr. Abdullahi Ganduje ya ce sun shirya tsaf domin kwace iko a jihar Rivers.
Abdullahi Ganduje ya ce a jihohin Kudu maso Kudu sun kwace ikon Cross River da Edo inda ya ce sun shiryawa jihar Rivers.
Asali: Legit.ng