'Idan Tinubu Ya Fadi, na Fadi': Awa 24 da Sukar Tinubu, Gwamnan PDP Ya Lashe Amansa

'Idan Tinubu Ya Fadi, na Fadi': Awa 24 da Sukar Tinubu, Gwamnan PDP Ya Lashe Amansa

  • Awanni 24 bayan gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori ya soki Bola Tinubu, ya sake yabonsa
  • Gwamnan a cikin wani bidiyo ya bukaci yan jiharsa su goyawa Tinubu baya kamar yadda suke yi masa
  • Sakataren yada labaran gwamnan, Festus Ahon ya ƙaryata cewa gwamnan ya soki Tinubu inda ya ce suna da kyakkyawar alaka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Delta - Gwamna Sheriff Oborevwori na jihar Delta ya yabawa salon mulkin shugaban kasa, Bola Tinubu.

Gwamnan ya bukaci yan Najeriya su marawa Tinubu baya domin kawo cigaba a Najeriya baki daya.

Gwamna ya lashe amansa bayan sukar Tinubu
Gwamna Sheriff Oborevwori na Delta ya bukaci ba Bola Tinubu goyon baya. Hoto: Sheriff Oborevwori, Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: UGC

Gwamnan Delta ya caccaki Bola Tinubu

Oborevwori ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da jaridar TheCable ta wallafa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan na zuwa ne kwana daya bayan gwamnan ya caccaki tsarin shugabancin Tinubu a Najeriya.

Kara karanta wannan

Kwana 1 ga barazanar Turji, an yi kazamar fada tsakanin yan bindiga, an rasa rayuka

A cikin kalamansa, Oborevwori ya ce babu wanda zai goyi bayan mulkin APC da ke cike da zalunci.

"Waye zai goyi bayan tsarin T-Pain domin kawo sauki a kasa?, wannan shi ne tsarin da Omo-Agege yake cewa zai kawo jihar Delta?"

- Sheriff Oborevwori

Gwamna ya yabawa salon mulkin Tinubu

Amma bayan awanni 24, an gano a cikin wani bidiyo yana yabon Tinubu kan cigaba a Najeriya.

Gwamnan ya ce samun nasarar Tinubu kaman shi ne cigabansa haka nan idan ya gaza samun nasara.

"Idan Tinubu ya yi rashin nasara, nima zan rasa nasara, Allah ya ba shi mukamin shugaban kasa kamar yadda ya ba ni na gwamna."
"Kamar yadda kuke goyon bayana, shi ma ku mara masa baya, saboda ba fata ba idan ya gaza nasara, nima na fadi."

- Sheriff Oborevwori

Da yake martani bayan yada cewa gwamnan ya soki Tinubu, sakataren yada labaran Oborevwori ya ce babu gaskiya a labarin.

Kara karanta wannan

"Zai lalubo hanya," Ministan Tinubu ya bayyana gwamnan da zai dawo APC

Festus Ahon ya ce Tinubu yana da kyakkyawar alaka da Gwamna Sheriff Oborevwori ba kamar yadda Leadership ta ruwaito ba.

Sanata ya alwashin ba APC jihar Delta

Kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ovie Omo-Agege ya sha alwashin kawo APC a Delta.

Wannan na zuwa ne bayan shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya ce a 2027 zai sake kwace Rivers ta dawo hannunsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.