2027: Duk da Adawar Dattawa, Wata Kungiyar Arewa Ta Goyi bayan Tazarcen Tinubu
- Kungiyar APC, reshen Arewa ta Tsakiya ta bayyana goyon bayanta ga Shugaba Bola Tinubu domin ya tsayawa takara a zaben 2027
- Wannan na zuwa ne yayin da kungiyoyin Arewa irinsu ACF da AYCF suka nuna rashin amincewarsu ga kudurin tazarcen Tinubu
- Sai dai kungiyar APC reshen Arewa ta Tsakiya ta ce gyran kasa, inganta tsaro da rabon mukamai sun isa a marawa Tinubu baya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Kungiyar APC ta Arewa ta Tsakiya ta goyi bayan shugaba Bola Ahmed Tinubu don ya sake tsayawa takara a 2027.
Kungiyar ta ce Shugaba Tinubu ya samar da damarmaki masu yawan gaske ga shiyyar Arewa ta Tsakiya tun shigarsa ofis a ranar 29 ga Mayu, 2023.
Kungiyar Arewa ta goyi bayan tazarcen Tinubu
Shugaban kungiyar, Alhaji Saleh Zazzaga, ya bayyana cewa yankin zai goyi bayan Tinubu a zaben shugaban kasa na 2027 da ke tafe, inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin wata sanarwa da ya fitar jim kadan bayan taron kungiyar a Abuja, Alhaji Saleh ya ce Arewa maso Gabas za ta rama halaccin da Tinubu ya yi mata a 2027.
Wannan na zuwa ne yayin da kungiyar Arewa Consultative Forum da matasanta (AYCF) suka nuna rashin goyon baya ga kudurin tazarcen Tinubu a zaben 2027.
A wata sanarwa, kungiyar ACF ta ce za ta goyi bayan dan Arewa ne kawai a zaben shugaban kasar Najeriya da ke tafe.
Kungiyar APC ta juyawa ACF, AYCF baya
Shi ma shugaban kungiyar AYCF, Alhaji Shettima Yerima, ya ce yankin Arewa yana nadamar goyon bayan Tinubu a zaben 2023.
Kungiyar AYC ta gargadi Tinubu cewa Arewa ba za ta saurare shi a zaben 2027 ma muddin gwamnatinsa ba ta inganta tattalin arziki ba.
Sai dai, kungiyar APC, reshen Arewa ta Tsakiya ta ce yankinta ya ci gajiyar mulkin Tinubu ta fannin gyare-gyaren kasa, rabon mukamai da inganta tsaro.
Tsadar rayuwa: ACF ta taso Tinubu a gaba
A wani labarin, mun ruwaito cewa dattawan Arewa sun nuna damuwa kan matsin tattalin arziƙi a Najeriya, suna danganta hakan ga wasu manufofin Shugaba Bola Tinubu.
Kungiyar dattawan ta ACF ta gargadi mahukunta da su gaggauta ɗaukar matakan magance matsalolin tattalin arziƙi domin gujewa ƙarin taɓarɓarewar halin rayuwa.
Asali: Legit.ng