Kano: Kusa a APC Ya Gargadi Sanata Kawu Sumaila kan Sukar Gwamnatin Tinubu
- Jigo a APC, AbdulMajeed Danbilki Kwamanda ya shawarci Sanata Kawu Sumaila da ya shigo jam'iyya mai mulkin kasa
- Danbilki Kwamanda ya shaida cewa matukar Kawu zai dawo APC, akwai babban yakinin cewa zai samu kujerar gwamna
- Ya bayyana cewa matukar Sanatan na NPP zai dawo APC ya nemi kujerar gwamna, sai ya guji caccakar gwamnatin Tinubu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Jigo a jam'iyyar APC reshen Kano, AbdulMajeed Danbilki Kwamanda ya shawarci Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu, Kawu Sumaila a kan alaka da gwamnatin Bola Tinubu.
Shawararsa na zuwa ne a kwanaki kadan bayan Sanata Kawu Sumaila na NNPP ya bayyana cewa ya na da alaka da gwamnatin tarayya da APC ke jagoranta.
A sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, AbdulMajeed Danbilki Kwamanda ya shawarci Kawu Sumaila da ya gaggauta dawowa jam'iyyarsa ta APC saboda nagartar da ya ke da ita.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jigon APC ya shawarci Kawu Sumaila
Makusancin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya shawarci Sanata Kawu Sumaila da cewa ya su na bukatarsa ya dawo jam'iyya mai mulki.
AbdulMajeed Danbilki Kwamanda ya kara da cewa;
"To mu na da wanda za mu dogara da shi, wanda zai iya cin gwamnan Kano, Kawu Sumaila, saboda mai alheri ne, mutumin kirki ne, ga shi ya na da ilimi guda biyu, ga na addini ga na boko."
Kusan APC ya soki masu adawa da kawu
Danbilki Kwamnada ya shawarci masu sukar Sanata Kawu Sumaila da su cigaba da shirmensu, yayin da su ke cigaba da nemansa ya dawo jam'iyyar.
"Kawu Sumaila, ba kashin yarwa ba ne, mu na tare da shi mun makalkale abinmu, kadara ce farar kadara, don haka duk abin da zai taso, wanda za a yi magana ba mu ba ka damar ka yi magana ba."
Ya shawarci Sanatan da ya yi gum da duk wasu abubuwa da gwamnatin Tinubu za ta yi, har sai an cimma manufar ya zama gwamnan Kano.
Sanata Kawu ya fadi alakarsa da APC
A baya mun ruwaito cewa Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu, Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila ya tabbatar da cewa ya na da alaka da jam'iyyar APC, musamman ta sama.
Sanata Kawu Sumaila ya bayyana cewa gwamnatin jihar Kano da jam'iyyar NNPP ne suka tsunduma shi yin alaka da APC, amma ba wai da kansa ya shiga cikin siyasar ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng