Tinubu: Wasu Ƴan Arewa Sun Bayyana Wanda Za Su ba Amanar Najeriya a 2027

Tinubu: Wasu Ƴan Arewa Sun Bayyana Wanda Za Su ba Amanar Najeriya a 2027

  • Kungiyar APC ta Arewa ta Tsakiya ta bayyana goyon baya ga tazarcen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027
  • Shugaban kungiyar, Saleh Zazzaga ya ce za su sake zaɓen Tinubu a karo na biyu saboda ayyukan da ya yi a shiyyar Arewa ta Tsakiya
  • Wannan dai na zuwa ne a lokacin da wasu ƴan Arewa suka fara juyawa Bola Tinubu baya tun kafin zuwan zaɓe

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Jam'iyyar APC reshen Arewa ta Tsakiya ta bayyana cewa ƴan Arewa za su sake marawa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu baya a zaɓen 2023.

Bayan wani taro da aka gudanar da Abuja, kungiyar ƴaƴan APC nanata cewa ƴan Arewa za su dangwalawa Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shugaban kasa na 2027.

Bola Tinubu.
Kungiyar APC a Arewa ta Tsakiya ta bayyana goyon bayan tazarcen shugaba Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinibu
Asali: Facebook

Hakan na kunshe a wata sanarwa da shugaban kungiyar ƴan APC na Arewa ta Tsakiya, Saleh Zazzaga ya fitar bayan gama taron ranar Talata, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Ana neman Obasanjo, IBB, Buhari, Jonathan su hadu, su kifar da Tinubu a 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

APC ta Arewa ta Tsakiya na tare da Tinubu

Ya ce ƙungiyar ƴaƴan APC ta yanke shawarar goyon bayan Tinubu ya yi takwas saboda gwamnatinsa ta ba Arewa ta Tsakiya damarmaki da kujeru masu tsoka.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar manyan Arewa ACF da matasan Arewa suka nuna adawa ƙarara da shirin tazarcen Bola Tinubu.

Amma a cewar kungiyar ƴan APC a Arewa ta Tsakiya, ta yanke goyon bayan Tinubu ne saboda yankin ya amfana da gwamnati mai ci.

Arewa ta amfana da mulkin Bola Tinibu

Saleh Zazzaga ya bayyana cewa shiryyar Arewa ta Tsakiya ta amfana da Shugaba Tinubu musamman ta ɓangaren ababen more rayuwa, naɗe-naɗe da sha'anin tsaro.

"Daga cikin abubuwan da muka tattauna a taron da ya gudana a karshen mako a Abuja, kungiyar ƴan APC ta Arewa maso Yamma ta yanke shawarar goyon bayan Tinubu a zaɓen 2027."

Kara karanta wannan

2027: Jam'iyyar APC ta yi zazzafan martani kan ziyarar Kwankwaso ga Obasanjo

“Babu wani shugaban kasa da ya kawo ayyukan ci gaba, samar da ababen more rayuwa a Arewa ta Tsakiya kamar Shugaba Tinubu.

Lukman ya ba manyan ƴan adawa shawara.

A wani labarin, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban APC, Salihu Lukman ya ce dole sai ƴan siyasa sun haɗa kai, su yiwa Tinubu taron dangi.

A cewar Salihu, ya kamata manyan siyasar ƙasar nan su dunkule wuri guda kuma su kirkiro sabuwar jam'iyya kafin 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262