2027: Jam'iyyar APC Ta yi Zazzafan Martani kan Ziyarar Kwankwaso ga Obasanjo
- Jam'iyyar APC ta bayyana cewa ba ta jin tsoron haɗin gwiwar Olusegun Obasanjo, Rabiu Kwankwaso da Peter Obi kan batun 2027
- APC mai rike da mulki ta ce Bola Tinubu yana da karfi kuma ya fi waɗannan jiga-jigan tasiri a siyasar da ake bugawa a halin yanzu
- Ta kuma fadi yadda Obasanjo ya goyi bayan ‘yan takara a baya kuma suka sha kaye a dalilin rashin ganin tasirinsa a siyasa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja, Nigeria - Jam’iyyar APC ta bayyana cewa ziyartar tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo da jiga-jigan adawa irin su Rabiu Kwankwaso suka yi ba zai tayar mata da hankali ba.
Jam'iyyar APC ta ce ko da Rabi'u Kwankwaso da Peter Obi za su hadu karkashin Obasanjo, hakan ba zai yi tasiri ba a siyasar Najeriya.
Bayanin ya fito ne daga bakin daraktan yada labaran APC, Bala Ibrahim yayin wata tattaunawa da Punch ta yi da shi a ranar Lahadi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Legit ta rahoto cewa Kwankwaso da tsohon gwamnan jihar Cross River, Donald Duke sun kai ziyara gidan Obasanjo a Abeokuta domin tattauna makomar siyasar Najeriya.
Martanin APC ga Olusegun Obasanjo
Daraktan yada labaran APC, Bala Ibrahim, ya ce duk da yana girmama Obasanjo, amma a siyasar da ake yi a yanzu, Tinubu ya wuce saninsa .
Bala Ibrahim ya ce Bola Tinubu ya wuce Obasanjo, Kwankwaso da Obi a siyasa, kuma haɗuwar su ba za ta kawo barazana ga mulkin APC ba.
Ya kara da cewa, a baya, Obasanjo ya goyi bayan ‘yan takarar da suka sha kaye, ciki har da Goodluck Jonathan da Peter Obi
APC ta ce sai 2031 Tinubu zai sauka
A cewar APC, mulkin Tinubu zai ci gaba har zuwa 2031, domin babu wani wanda zai iya fitar da APC daga Aso Rock a zaben 2027.
"Ko da za su cigaba da taruwa daga yau har abada ba za su zama barazana ga gwamnatin APC ba"
- Bala Ibrahim
Tsohon shugaban kasa Obasanjo ya shahara da sukan mulkin Tinubu, yana bayyana damuwa kan karuwar bashin ƙasa da zargin cin hanci.
Obasanjo ya bukaci korar shugaban INEC
A wani rahoton, kun ji cewa Cif Olusegun Obasanjo ya yi kakkausar suka ga shugabannin hukumar INEC a Najeriya.
Olusegun Obasanjo ya bukaci gwamnatin tarayya ta kori shugaban INEC na kasa, Farfesa Mahmood Yakubu da shugabannin hukumar a jihohi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng