"Ban da Karba Karba": Shekarau Ya Fadi Hanyar Samar da Shugaban Kasa a 2027

"Ban da Karba Karba": Shekarau Ya Fadi Hanyar Samar da Shugaban Kasa a 2027

  • Malam Ibrahim Shekarau ya yi magana kan abin da ya dace ƴan Najeriya su kalla a wajen yin zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027 da ke tafe
  • Tsohon gwamnan na jihar Kano ya bayyana cewa la'akari da yankin da shugaban ƙasa zai fito ba shi ba ne mafita ga ƴan Najeriya
  • Shekarau ya nuna cewa kamata ya yi ƴan Najeriya su damu da nagartar ƴan takarar da jam'iyyu za su gabatar ba wai yankin da suka fito ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, ya yi magana kan zaɓen shekarar 2027 da ke tafe.

Ibrahim Shekarau ya bayyana cewa ya kamata ƴan Najeriya su daina la'akari da yankin da shugaban ƙasa zai fito.

Shekarau ya ba 'yan Najeriya shawara kan zaben 2027
Shekarau ya bukaci 'yan Najeriya su duba nagarta a zaben 2027 Hoto: Malam Ibrahim Shekarau
Asali: Facebook

Shekarau ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da tashar Channels tv a ranar Lahadi, 15 ga watan Disamban 2027.

Kara karanta wannan

PDP ta ba Jonathan damar gwabzawa da Tinubu a 2027? Jam'iyyar ta yi bayani

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wace shawara Shekarau ya ba da kan zaɓen 2027?

Tsohon sanatan ya bayyana cewa kamata ya yi ƴan Najeriya su damu da nagartar shugaban ƙasarsu, maimakon yankin da ya fito, tun daga lokacin zaɓe mai zuwa a 2027.

Ibrahim Shekarau ya bayyana cewa muhawarar da ake yi kan yankin da shugaban ƙasa zai fito, ba ta da wani tasiri a wajen mulki.

"Ya kamata dukkanin jam'iyyun su fito da tsare-tsarensu ta yadda za su yi zaɓi mai kyau. Amma domin ƴan Najeriya su yi zaɓinsu, abin da ya kamata mu damu shi ne waɗanne irin ƴan takara jam'iyyun suka gabatar."
"Ƙalubalen mu shi ne dukkanin jam’iyyun su ba ƴan Najeriya nagartattun ƴan takara, ta yadda za mu zaɓi wanda ya fi cancanta. Amma idan aka ba mu dukkanin baragurbi, za mu zaɓi mafi alheri daga cikinsu."

- Ibrahim Shekarau

Shekarau ya faɗi sirrinsa

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya fito ya bayyana wani sirrinsa wanda ba a san da shi ba.

Tsohon sanatan ya bayyana cewa abin yake da shi a asusunsa kafin tsayawa takarar gwamnan Kano, bai kai N100,000 ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng