Sagagi Ya Fadi Yadda Abba Kabir Yake bayan Zargin Gwamnan da Jin Zugar Mutane

Sagagi Ya Fadi Yadda Abba Kabir Yake bayan Zargin Gwamnan da Jin Zugar Mutane

  • Shehu Wada Sagagi ya bayyana irin abubuwan da ya koya yayin zama da Gwamna Abba Kabir Yusuf
  • Wada Sagagi ya ce sabanin abubuwan da ake yaɗawa cewa Abba Kabir yana jin zuga kwata-kwata ba gaskiya ba ne
  • Hakan na zuwa ne kwanaki uku bayan cire Sagagi a muƙamin shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin Kano

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Tsohon shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin Kano, Shehu Wada Sagagi ya magantu kan halin Gwamna Abba Kabir.

Wada Sagagi ya ce bai san wani abu daga Abba ba sai alheri saboda abin da ke bakinsa shi ne a zuciyarsa.

Sagagi ya fadi halayen Abba Kabir
Shehu Wada Sagagi ya magantu kan halayen Gwamna Abba Kabir a Kano. Hoto: Kwankwasiyya Reporters.
Asali: Facebook

Sagagi ya yabawa kwazon Abba Kabir

Hakan na kunshe ne a cikin wani faifan bidiyo da Nuhu Sani Dambazau ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

"Dole mu farka," Sarki Muhammadu Sanusi II ya haɗarin da Arewa ke ciki a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin bidiyon, Sagagi ya bayyana yadda Abba Kabir ya kasance mai kwazon aiki duk yawan rubutu sai ya bi shi layi-layi.

Ya ce lokacin da Abba Kabir ya ba shi mukamin ya ba shi shawarwari da cewa dole sai ya yi hakuri da aikin.

Sagagi ya musanta rade-radi kan Abba Kabir

"Da yana daukar zuga ai da ba zan yi ko da wata a kan wannan kujerar ba, wallahi ba zan yi ba, duk fada ne."
"Wato ba su fahimci mai girma gwamna ba ne kwata-kwata wallahi, maganar yan uba kuma ai duk wanda ke da wannan rufin asiri sai Allah ya kawo masa yan hassada."
"Ai tsari ne na kafofin sadarwa mutum bai san ka ba ya yanke maka hukunci, a lahira mutane suna ji suna gani za su dauki ladansu su ba Sagagi."

- Shehu Wada Sagagi

Sagagi ya yi wa Abba Kabir godiya

A wani labari mai kama da wannan, Alhaji Shehu Wada Sagagi ya yi godiya ga Abba Kabir kan damar da ya ba shi na rike muƙamin shugaban ma'aikatan fadar gwamnati.

Kara karanta wannan

Kano: Sagagi ya magantu bayan rasa muƙamin CoS, ya tura sako ga Abba Kabir

Wada Sagagi ya ce ba zai taba yin butulci ba kuma yaki tare da Gwamna Abba wallahi yanzu ma aka fara.

Hakan ya biyo bayan sauke shi daga mukaminsa bayan Abba Kabir ya yi garambawul a gwamnatinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.