Kano: Sagagi Ya Magantu bayan Rasa Muƙamin CoS, Ya Tura Sako ga Abba Kabir

Kano: Sagagi Ya Magantu bayan Rasa Muƙamin CoS, Ya Tura Sako ga Abba Kabir

  • Alhaji Shehu Wada Sagagi ya yi godiya ga Abba Kabir kan damar da ya ba shi na rike muƙamin shugaban ma'aikatan fadar gwamnati
  • Wada Sagagi ya ce ba zai taba yin butulci ba kuma yaki tare da Gwamna Abba wallahi yanzu ma aka fara
  • Hakan ya biyo bayan sauke shi daga mukaminsa bayan Abba Kabir ya yi garambawul a gwamnatinsa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Tsohon shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin Kano, Shehu Wada Sagagi ya magantu bayan cire shi da aka yi.

Wada Sagagi ya godewa Gwamna Abba Kabir game da damar da ya ba shi da cewa lokacinsa ne ya kare.

Wada Sagagi ya magantu bayan rasa kujerar shugaban ma'aikatan fadar gwamnati
Bayan rasa mukaminsa a gidan gwamnati, Shehu Wada Sagagi ya godewa Abba Kabir. Hoto: Kwankwasiyya Reporters.
Asali: Facebook

Sagagi ya tabbatar yana tare da Abba

Hakan na kunshe a cikin wani faifan bidiyo da Nuhu Sani Dambazau ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Yadda mai magana da yawun Gwamna Abba ya tsira daga kamun 'yan sanda

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin bidiyo, Wada Sagagi ya ce suna nan daram tare da mai girma Gwamna Abba Kabir a kowane hali.

"Ai ba butulu ba ne ni, kullum ina fada yau an baka dama, gobe idan aka cire ka, ka ce a'a kai sai dai kai."
"Ai ba cewa aka yi an kore ni daga NNPP ba ko Kwankwasiyya muna nan daram kuma gwagwarmaya tare da mai girma Gwamna yanzu aka fara."
"Ko mahaukaci ya san muna son gwamna kuma yana sonmu, ai lokacin da aka ba mu wasu ne suka yi hakuri, meye a ciki yanzu idan an ce ku yi hakuri."

- Shehu Wada Sagagi

Sagagi ya ce ba zai yi butulci ba

Rahotanni sun tabbatar da cewa Wada Sagagi ya yi hirar ce domin yin raddi ga yan adawa wanda ya shirya yi kafin a sallame shi.

Sai dai duk da cire a muƙamin da aka yi, bai hana ya gabatar da raddin ba inda ya ce ba zai taba yin butulci ba.

Kara karanta wannan

Malamin Musulunci ya roki afuwar al'umma kan kiran Sanusi II da tsohon sarki

Sanusi Bature ya magantu kan yunkurin kama shi

Kun ji cewa Sanusi Bature Dawakin Tofa wanda yake magana da yawun bakin gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi magana kan yunƙurin cafke shi.

Mai magana da yawun bakin gwamnan na Kano ya bayyana cewa ya fake a gidan gwamnatin jihar domin ka da ƴan sanda su kama shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.