Baraka a NNPP: Kawu Sumaila Ya Fadi Dalilin Yin Alakarsa da Jam'iyyar APC
- Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila ya yi magana kan raɗe-raɗin da ake cewa yana da alaƙa da jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya
- Kawu Sumaila mai wakiltar Kano ta Kudu ya bayyana cewa tabbas yana da alaƙa da APC amma ta sama
- Sai dai, sanatan ya bayyana cewa gwamnatin Kano da jam'iyyar NNPP ne suka jawo yake yin alaƙa da APC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu, Abdulrahman Kawu Sumaila, ya taɓo batun alaƙar da ke tsakaninsa da jam'iyyar APC.
Kawu Sumaila wanda aka zaɓa ƙarƙashin inuwar jam'iyyar NNPP ya amsa cewa tabbas yana da alaƙa da APC a sama.
Sanatan ya bayyana hakan yayin wata hira wacce wani mai suna Dan Sumaila ya sanya a shafinsa na TikTiok.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa Kawu Sumaila ke alaƙa da APC?
Kawu Sumaila ya bayyana cewa gwamnatin jihar Kano da jam'iyyar NNPP ne suka tsunduma shi yin alaƙa da APC.
"Wallahi idan wasu suna magana kan alaƙarmu da gwamnatin APC ko an rufe baki na, ko an yi miye, wallahi kawai dariya nake yi."
"Na yarda yanzu ina da alaƙa da gwamnatin APC ta sama. Amma Allah yana sama yana kallo, Allah yana ji, waɗanda suka tsunduma ni wannan alaƙa, jam'iyyar NNPP da gwamnatin jihar Kano ne."
- Kawu Sumaila
Menene alaƙar Kawu Sumaila da Gwamna Abba
Kawu Sumaila ya bayyana cewa har yanzu yana ganin girman gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf da jagoran NNPP na ƙasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
"Wallahi har zuwa gobe ina girmama shi. Ni ban san wani abu da ya yi wanda ya nuna cewa ba ya ganin girma na ba. Ina girmama shi a matsayinsa na jagora wanda muka haɗu muka kafa wannan alkhairi."
Kawu Sumaila
Kawu Sumaila ya ba Gwamna Abba shawara
A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila ya ba da shawara ga gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf.
Sanatan mai wakiltar Kano ta Kudu ya buƙaci gwamnan da ya kasance mai yin gaskiya da adalci ga mutanen jihar ba tare da nuna bambancin siyasa ba.
Asali: Legit.ng