Bayan Kalaman Ganduje, Sanata Ya Yi Alkawarin Kawo Jihar PDP Dungurungum ga APC

Bayan Kalaman Ganduje, Sanata Ya Yi Alkawarin Kawo Jihar PDP Dungurungum ga APC

  • Tsohon mataimakin shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ovie Omo-Agege ya bugi kirji kan zaben 2027
  • Sanata Omo-Agege da Hon. Erhiataka Suenu-Ibori sun sha alwashin kwace jihar Delta daga hannun PDP zuwa APC
  • Wannan na zuwa ne bayan shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya ce a 2027 zai sake kwace Rivers ta dawo hannunsu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Delta - Tsohon mataimakin shugaban Majalisar Dattawa, Ovie Omo-Agege ya sha alwashin kawo jam'iyyar APC a jihar Delta.

Omo-Agege da kuma yar Majalisar Wakilai, Erhiataka Suenu-Ibori sun yi alkawarin kifar da jam’iyyar PDP a jihar.

Sanata ya sha alwashin kawo jihar PDP ga APC a zaɓe
Sanata Ovie Omo-Agege da yar Majalisar sun yi alkawarin kawo jihar Delta ga APC. Hoto: Dr. Abdullahi Ganduje.
Asali: Facebook

Sanata ya tabbatar da karfin APC a Delta

Sanata Omo-Agege da Suenu-Ibori sun bayyana hakan ne a karshen mako bayan da yar majalisar ta sauya sheƙa daga PDP zuwa APC, cewar Leadership.

Kara karanta wannan

Bayan cika bakin Ganduje, an dakatar da shugaban jam'iyyar APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sun tabbatar da cewa suna da ƙarfin cimma wannan buri musamman duba da cewa da karfin da Suenu-Ibori ta fito da shi.

Hon. Suenu-Ibori, wadda ke wakiltar mazaɓar Ethiope ta Yamma da Gabas ta ce duk da kasancewarta a PDP a baya, ruhinta yana tare da APC.

Yar Majalisar ta tabbatar da cewa haske da iskar da ke zuwa za su taimaka wurin tarwatsa PDP, The Nation ta ruwaito.

Yar Majalisa ta kwantarwa yan APC hankali

“PDP ta mutu kuma an binne ta a jihar Delta, mun zo nan ne domin mu tabbatarwa mutane cewa APC ta cika kuma yanzu gida na dawo."
"Sun yi ƙoƙarin tsayawa gaba na, amma ni ɗiyar zaki ce, babu wanda zai iya tsayawa gabana, babu wanda zai iya ture ni."
“Jagoranmu, Sanata Ovie Omo-Agege yanzu ya samu mutanen da za su kai mazaɓar Ethiope ga APC, ku kwantar da hankalinku, muna da ƙarfin cimma wannan buri."

Kara karanta wannan

2027: Ana kukan mulkinsu, Ganduje ya ce zai kwace jihar da APC ba ta taɓa mulki ba

- Hon. Suenu-Ibori

Sanata Ovie Omo-Agege ya bayyana farin cikinsa na karɓar Suenu-Ibori tare da hangen nesa da ta yi wajen shiga APC.

Ganduje ya shirya kwace jihar Rivers

Mun ba ku labarin cewa shugaban jam'iyyar APC a Najeriya, Dr. Abdullahi Ganduje ya ce sun shirya tsaf domin kwace iko a jihar Rivers.

Ganduje ya ce a jihohin Kudu maso Kudu sun kwace ikon Cross River da Edo inda ya ce sun shiryawa Rivers a zaben 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.