2027: Kwankwaso da Tsohon Gwamna Sun Ziyarci Obasanjo, Sun Tattauna Batutuwan Siyasa
- A ranar Asabar 14 ga watan Disambar 2024, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya kai ziyara jihar Ogun
- Sanata Kwankwaso ya kai ziyara ta musamman har gidan tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo a Abeokuta
- Wannan na zuwa ne yayin da ake ta rade-radin yan adawa na kokarin hada kai domin tunkarar zaben 2027 da Bola Tinubu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Ogun - Jagoran siyasar Kano, Sanata Rabi'u Kwankwaso ya kai ziyara ga tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo.
Sanata Kwankwaso ya gana da Cif Obasanjo na tsawon lokaci a birnin Abeokuta da ke jihar Ogun.
Kwankwaso ya kai ziyara ta musamman ga Obasanjo
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Kwankwaso ya wallafa a shafin X a daren jiya Asabar 14 ga watan Disambar 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwankwaso ya ziyarci tsohon shugaban kasar tare da rakiyar tsohon gwamnan Cross River kuma abokinsa, Donald Duke.
Sanata Kwankwaso ya ce sun tattauna batutuwa masu muhimmanci game da makomar siyasar Najeriya.
A cikin tattaunawar har ila yau, akwai sha'anin shugabanci da sauran matsaloli da suka addabi Najeriya.
Menene Sanata Kwankwaso ya tattauna da Obasanjo?
"Na ji dadin kasancewa tare da abokina, Mai Girma, Donald Duke, da wasu abokai domin kai ziyara ta girmamawa ga tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo a gidansa da ke Abeokuta."
"Tattaunawar mu ta karkata kan manyan batutuwan kasa, ciki har da makomar siyasa da shugabanci a Najeriya."
"Mu na godiya ga Baba bisa goyon bayanka a ko da yaushe da kuma karimcinka."
- Sanata Rabi'u Kwankwaso
NNPP ta magantu kan jagorancin Kwankwaso
Kun ji cewa shugabannin NNPP na jihohi shida sun musanta raɗe-raɗin da ke yawo cewa jam'iyyar ta dare gida biyu saboda rikici.
A wata sanarwa da suka fitar a birnin Port Harcourt, sun ce NNPP a dunƙule take karƙashin jagorancin Ajuji Ahmed da Sanata Rabiu Kwankwaso.
Sun tabbatar da cewa tsagin Agbor Major da sauran ƴan tawagarsa ba ƴan NNPP ba ne domin an jima da korarsu daga jam'iyyar baki dayanta.
Asali: Legit.ng