2027: Ana Kukan Mulkinsu, Ganduje Ya Ce Zai Kwace Jihar da APC ba Ta Taɓa Mulki ba

2027: Ana Kukan Mulkinsu, Ganduje Ya Ce Zai Kwace Jihar da APC ba Ta Taɓa Mulki ba

  • Shugaban jam'iyyar APC a Najeriya, Dr. Abdullahi Ganduje ya ce sun shirya tsaf domin kwace iko a jihar Rivers
  • Ganduje ya ce a jihohin Kudu maso Kudu sun kwace ikon Cross River da Edo inda ya ce sun shiryawa Rivers
  • Tsohon gwamnan Kano ya bukaci yan APC da masu ruwa da tsaki su goya musu baya domin cimma burin da suka sanya a gaba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Rivers - Shugaban jam'iyyar APC, Dr Abdullahi Ganduje ya sha alwashin kwace jihar Rivers.

Tsohon gwamnan Kano ya bayyana cewa jam’iyyarsa za ta karbe ikon jihar a zaben shekarar 2027 mai zuwa da za a yi.

Ganduje ya sha alwashin kwace Rivers a 2027
Shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya sha alwashin karbe iko a jihar Rivers a zaben 2027. Hoto: Senator Magnus Abe.
Asali: Facebook

Ganduje ya shawarci yan APC a Rivers

Ganduje ya fadi haka ne yayin rantsar da Cif Tony Okocha da wasu mutum 22 a matsayin shugabannin jam’iyyar APC a jihar, cewar Punch.

Kara karanta wannan

A karshe, Jonathan ya samu damar gwabzawa da Tinubu a 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dr. Ganduje ya bukaci ’yan jam'iyyar APC su yi duk mai yiwuwa don ganin jam’iyyar ta lashe zaben gwamna na 2027.

Shugaban APC ya ce yankin Kudu maso Kudu da galibi PDP ke mulki tana cigaba da rushewa kasancewar APC ta kwace iko a jihohin Cross River da Edo.

Ya kara da cewa jihar Rivers ita ce jihar da ke gaba a jerin inda APC za ta kwace a zaben gwamna na 2027.

'Rivers ce muka sanya a gaba' - Ganduje

“Kun fito ne daga yankin Kudu maso Kudu da jam'iyyar PDP ta dade tana rike da yankin."
"Amma kun sani sosai cewa a lokacin gwamnatin Buhari, mun samu damar kwace jihar Cross River daga hannun PDP."
"A karkashin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu kuwa, mun yi nasara a zaben jihar Edo daga cikin jihohi shida a yankin, mun kwato biyu."
"Jihar Rivers ita ce gaba a jerinmu, Rivers mun zo gare ku, Rivers kun kusa zama na APC."

Kara karanta wannan

Jagoran PDP ya fadi wanda ake amfani da shi domin rusa jam'iyyar adawa

- Abdullahi Umar Ganduje

Bayan korafin Ganduje, kotu ta yi hukunci

Kun ji cewa Babbar Kotun jihar Kano ta yi zama kan korafin shugaban APC, Abdullahi Ganduje game da kakakin Gwamna Abba Kabir.

Kotu ta haramta kama Sanusi Bature Dawakin-Tofa kan zargin cewa ya kitsa dakatar da Ganduje a gundumarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.