Rai ya yi halinsa: Dan Majalisa Mai Ci Ya Yi Bankwana da Duniya a Abuja

Rai ya yi halinsa: Dan Majalisa Mai Ci Ya Yi Bankwana da Duniya a Abuja

  • Gwamnatin jihar Kogi ta yi babban rashi bayan sanar da rasuwar dan Majalisar dokokinta a yau Asabar
  • An tabbatar da rasuwar marigayi Hon. Enema Paul wanda ya yi bankwana da duniya a asibitin Abuja
  • Kakakin Majalisar, Hon. Aliyu Umar Yusuf ya bayyana marigayin a matsayin mutumin kirki kuma mai kishin kasa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kogi - Tsohon mataimakin kakakin Majalisar dokokin jihar Kogi, Hon. Enema Paul ya rasu.

Rahotanni sun bayyana cewa Hon Enema ya mutu a wani asibiti mai zaman kansa da ke Abuja da sanyin safiyar ranar Asabar 14 ga watan Disambar 2024.

Dan Majalisar jihar Kogi ya riga mu gidan gaskiya
Dan Majalisa a jihar Kogi, Hon. Enema Paul ya rasu. Hoto: Enema Paul.
Asali: Facebook

Dan Majalisa a jihar Kogi ya rasu

Tribune ta tabbatar cewa marigayin ya rasu ne sakamakon wata rashin lafiya da ba a bayyana ba.

Kara karanta wannan

Majalisa ta fito da bayani kan rage karfin ikon Lamidon Adamawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kafin rasuwarsa, Hon. Paul shi ne ke wakiltar mazabar Okura wanda sauka daga mukaminsa na mataimakin kakakin Majalisar saboda matsalar rashin lafiya.

An maye gurbinsa a watan Disambar 2023 da Hon. Comfort Ojoma wacce ke wakiltar mazabar Ibaji a jihar.

Majalisar ta mika sakon ta'azziya ga iyalansa

Kakakin majalisar, Hon. Aliyu Umar Yusuf ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin wanda rasuwarsa ta girgiza al'umma.

A cikin wata sanarwa da hadimin kakakin Majalisar ya fitar, ya bayyana marigayin a matsayin aboki kuma mutum mai saukin kai da ke aiki tare da kowa.

Hon. Umar ya ce marigayi Paul ya zama abin koyi wajen jajircewa kan hadin kan jihar da kokarin kawo dokoki masu amfani don cigaban al’umma baki daya.

Ya ce marigayin mutum ne mai kishin addini wanda ya zamo abin koyi wajen nuna soyayya tsakanin addinai da kuma kishin darajar iyali.

Kakakin Majalisar ya yi addu’ar Allah ya ba iyalan mamacin da ’yan Majalisar hakurin jure wannan babban rashi.

Kara karanta wannan

Majalisar tarayya za ta binciki yadda gwamnatin Buhari ta kashe bashin $232m

Shugaban karamar hukumar ya rasu a Niger

A baya, kun ji cewa, jihar Neja ta yi babban rashi bayan sanar da rasuwar shugaban ƙasar hukumar Katcha, Danlami Abdullah Saku rasuwa.

Danlami ya rasu ne sakamakon hatsarin motar da ya rutsa da shi a titin Minna-Suleja da misalin karfe 7:00 na daren ranar Talata, 10 ga watan Disamba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.