Bayan ba Jonathan Damar Takara, 'Yan Adawa Sun Fara Sabon Shirin Hadaka

Bayan ba Jonathan Damar Takara, 'Yan Adawa Sun Fara Sabon Shirin Hadaka

  • Jam’iyyun PRP da ADC sun fara tattaunawar haɗin kai domin ƙalubalantar jam’iyyar APC mai mulki a 2027
  • PRP da ADC sun zargi Muhammadu Buhari da Bola Tinubu da assasa talauci ta hanyar manufofi marasa amfani
  • Shugabannin jam’iyyun biyu sun bayyana cewa haɗin gwiwar da suke kokarin yi zai kawo sauyi mai ma’ana ga ƙasar nan

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja, Nigeria - Jam’iyyun PRP da ADC sun fara tattaunawa kan haɗa kai domin ƙalubalantar mulkin jam’iyyar APC a babban zabe mai zuwa.

Shugabannin jam’iyyun biyu sun zargi tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari da shugaban ƙasa mai ci, Bola Ahmed Tinubu, da haifar da matsanancin talauci a Najeriya.

Tinubu
PRP da ADC sun zargi Buhari da Tinubu da kakaba talauci a Najeriya. Hoto: Bayo Onanuga|Bashir Ahmad
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa jam'iyyun sun yi bayani ne a wani taron manema labarai da suka gudanar a Abuja ranar Juma’a.

Kara karanta wannan

Yadda dakarun sojoji suka hallaka 'yan ta'adda 181 yayin artabu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yayin taron, shugabannin PRP da ADC sun bayyana cewa talauci ya samo asali ne daga cin hanci da rashawa da sanya manufofin da ba su da amfani ga talakawa.

Manufofin haɗin kan PRP da ADC

Shugaban PRP, Dr Falalu Bello ya bayyana cewa sun fara tattaunawa domin haɗa kai tare da yin aiki tare da wasu jam’iyyun da suke son fitar da Najeriya kunya.

Dr Falalu Bello ya ce haɗin kan zai taimaka wajen ƙirƙirar dabarun magance matsalolin tattalin arzikin da ƙasar ke fama da su a halin yanzu.

Punch ta wallafa cewa Dr Bello ya jaddada cewa tun bayan dawowar mulkin dimokuraɗiyya a 1999, Najeriya ke fama da matsalolin tattalin arziki.

Managar cin hanci da rashawa a Najeriya

Shugaban ADC, Ralph Nwosu, ya zargi jam’iyyun APC da PDP da ƙirƙirar yanayin da cin hanci ya zama ruwan dare.

Kara karanta wannan

Batutuwa 30 sun jawo taron ECOWAS a Najeriya, ministoci sun hallara a Abuja

Ya ce cin hanci da rashawa ya yi katutu har ya zama abin alfahari, wanda hakan ke ƙara lalata ƙasa da rage amana tsakanin gwamnati da al’umma.

Lokacin kawo sauyi ya yi inji PRP da ADC

Shugabannin jam’iyyun biyu sun bayyana cewa babu wani lokaci mafi dacewa da za a haɗa kai domin ceto ƙasa kamar yanzu.

Sun kuma yi kira ga al’ummar Najeriya su rungumi wannan yunƙurin domin inganta goben 'yan kasa.

An ba Jonathan damar takara a 2027

A wani rahoton, kun ji cewa jam’iyyar PDP ta bukaci tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya tsaya takarar shugaban kasa a 2027.

PDP ta bayyana cewa yana da muhimmanci shugaba Jonathan ya ci gaba da ayyukan da ya fara a lokacin mulkinsa idan ya dawo a 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng