“Abin da Ya Sa Abba Ya Kori Sakataren Gwamnati, Sagagi da Kwamishinoni 5 a Kano”

“Abin da Ya Sa Abba Ya Kori Sakataren Gwamnati, Sagagi da Kwamishinoni 5 a Kano”

  • Adnan Mukhtar Adam Tudunwada ya yi fashin baki a kan matakan da Abba Kabir Yusuf ya dauka a gwamnatinsa
  • ‘Dan siyasar ya ce gwamnan jihar Kano ya hakura ya sallami mutanen da Rabiu Kwankwaso bai gamsu da su ba
  • A bangare guda kuma, gwamnatin Abba ta tsige wasu na kusa da Kwankwaso wanda shi ne ubangidansa a siyasa

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kano - Adnan Mukhtar Adam Tudunwada matashin ‘dan siyasa ne kuma malamin jami’a, ya yi magana a game da siyasar jihar Kano.

Malam Adnan Mukhtar Adam Tudunwada ya tofa albarkacin bakinsa bayan gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi sauye-sauye a gwamnati.

Abba.
Gwamnan jihar Kano ya kori manyan jami'an gwamnati 7 Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Adnan ya yi magana kan siyasar Abba da Kano

A wasu maganganu da ya rika yi a shafukansa na Facebook da X, Adnan Mukhtar Adam Tudunwada ya bayyana ra’ayoyinsa a fili.

Kara karanta wannan

Hadimin Gwamna Abba ya fito da abin da ya gani wajen Baffa Bichi da aka tsige

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

‘Dan siyasar ya yi ikirarin Dr Abdullahi Baffa Bichi ya sadaukar da rayuwarsa ga gwamnatin NNPP musamman a lokacin da ake shari’a.

Adnan ya na zargin cewa ubangidan gwamnan Kano ya matsa sai da aka tsige Dr Baffa Bichi daga kujerar sakataren gwamnati ba ciwo ba.

Abba ya tsaya da kafarsa a jihar Kano

Bai tsaya nan ba, Adnan Tudunwada ya ce a gefe guda, gwamna ya yi waje da Shehu Wada Sagagi wanda Rabiu Kwankwaso ya kawo.

A cewarsa, an kawo tsohon shugaban na PDP ne saboda a sa wa Abba ido a gidan fadar mulki, zargin da gwamnatin Abba ta karyata shi.

Abba ya taba mataimakin gwamnan Kano

Da yake karin bayani a shafin nasa, tsohon ‘dan takaran majalisar ya tabo zancen canza kwamishinan harkokin kananan hukumomi.

Malamin jami’an yake cewa da gan-gan aka maida mataimakin gwamna zuwa ma’aikatar ilmi mai zurfi saboda badakalar Novomed.

Kara karanta wannan

Baffa Bichi ya bayyana dalilin Abba na sauke shi daga sakataren gwamnatin Kano

Idan ikirarin ya tabbata, babu cikakkiyar jituwa tsakanin Abba da Aminu Abdussalam.

Bayaninsa ya nuna gwamnan ya yi waje da wasu mutanen Kwankwaso sannan kuma ya tsige wadanda madugun Kwankwasiyyar bai kuna.

Duk da matakin ya taba irinsu Abbas Sani Abbas, gwamnan ya sallami manyan kwamishinoni irinsu Ibrahim Jibril da Halili Dantiye.

Ana kewar rabuwa da Baffa Bichi

Ana da labari cewa Mai taimakawa gwamnan Kano, Salisu Yahaya Hotoro, ya yi magana a kan tsige Abdullahi Baffa Bichi da aka yi.

Hadimin gwamnan ya ce ya so Allah SWT ya bar shi da cikakkiyar lafiya da kwarin jiki domin ya yi aiki amma hakan bai samu ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng