Hadimin Gwamna Abba Ya Fito da Abin da Ya Gani wajen Baffa Bichi da Aka Tsige

Hadimin Gwamna Abba Ya Fito da Abin da Ya Gani wajen Baffa Bichi da Aka Tsige

  • Da Abba Kabir Yusuf ya tashi yin tankade da rairaya a gwamnati, ya yi waje da Abdullahi Baffa Bichi
  • Salisu Yahaya Hotoro yana cikin masu ba gwamna shawara, ya yabi Bichi wanda aka tsige a makon nan
  • Tun da Abba Kabir Yusuf ya nada shi, Hotoro ya nuna babu abin da suka gani wajen shi illa alherai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kano - A ranar Alhamis dinnan gwamna Abba Kabir Yusuf ya sallami wasu manyan jami’an gwamnatinsa a jihar Kano.

Wadanda sauye-sauyen suka shafa sun hada da sakataren gwamnati, shugaban ma’aikatan fada da kwamishinoni biyar.

Baffa Bichi
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tsige Dr. Abdullahi Baffa Bichi Hoto: Abba Kabir Yusuf/Dr. AB Baffa Bichi
Asali: Facebook

"Allah Sarki Abdullahi Baffa Bichi"

Wani daga cikin hadiman Alhaji Abba Kabir Yusuf ya yi magana bayan samun labarin an tsige Abdullahi Baffa Bichi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Salisu Yahaya Hotoro ya yi amfani da shafinsa na Facebook, babu abin da yake yi sai yabon Dr. Abdullahi Baffa Bichi.

Kara karanta wannan

“Abin da ya sa Abba ya kori Sakataren gwamnati, Sagagi da kwamishinoni 5 a Kano”

Mai taimakawa gwamnan a harkokin sada zumunta na zamani ya bayyana cewa ya so a ce Bichi ya iya rike kujerarsa.

Menene ya jawo aka kori Baffa Bichi?

Hadimin gwamnan yake cewa sai dai rashin lafiya ta tasa tsohon sakataren gwamnatin a gaba, dole ya bar matsayinsa.

Shi dai Hotoro ya ce bai san komai game da Bichi ba sai alheri a tsawon lokacin da ya yi a kujerar sakataren gwamnati.

Malam Hotoro ya koka game da yadda rashin lafiya ta jawo aka rabu da shi, yake cewa su na yi masa fatan alheri a rayuwa.

Maganar Hotoro a kan tsige Baffa Bichi

"Allah sarki SSG Dr. Ab Baffa Bichi, har ga Allah naso a ce Allah ya bar shi da cikakkiyar lafiya da kwarin jiki ta yadda zai iya taimakawa a samarwa jihar Kano cigaba amma Allah bai nufa ba.
"A iya zaman da nayi da mutumin nan da sanin da nayi masa Wallahi alkairinsa kawai na sani, mutum ne mai son taimako da kokarin samar da hanyoyin cigaba.

Kara karanta wannan

'Ba ku da hankali ne': Akpabio ga masu fada da Ministan Tinubu, ya jero dalilansa

"Za mu kasance masu yi masa fatan alkairi da fatan samun cikakkiyar lafiya, jihar Kano za ta ci gaba da tunawa da kai a matsayin daya daga cikin gwaraza kuma hazikan mutane masu kishinta."
"Ya Allah ka wadata wannan bawa naka da ingantacciyar lafiya, ka kara masa kwarin gwiwa ka bashi kariya a duk inda ya tsinci kansa."

- Salisu Yahaya Hotoro

Bichi da batun Abba tsaya da kafarka

Kwanaki an ji labari cewa an zargi Dr. Abdullahi Baffa Bichi da hannu wajen fito da kungiyar Abba tsaya da kafarka, amma ya karyata batun.

Ana ganin tsohon shugaban na hukumar TETFund wanda har ya taba zuwa kasar waje domin ganin likitoci yana cikin ‘yan a mutun gwamna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng