Kwana 1 da Korar na Kano, Wani Sakataren Gwamnatin Jiha Ya Ajiye Aikinsa a Arewa
- Rahotanni da muke samu sun tabbatar da cewa sakataren gwamnatin jihar Bauchi ya yi murabus daga mukaminsa
- Tsohon sakataren gwamnatin, Ibrahim Kashim ya ajiye aikinsa ne a yau Juma'a 13 ga watan Disambar 2024
- Wannan na cikin sanarwa da hadimin Gwamna Bala Mohammed ya fitar inda aka naɗa sakataren rikon kwarya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Bauchi - Sakataren Gwamnatin jihar Bauchi (SSG), Ibrahim Kashim ya yi murabus daga mukaminsa nan take.
Kashim bai bayyana dalilin ajiye aikin ba sai dai ana hasashen zai tsaya takarar gwamna a zaɓen 2027.
Menene dalilin musabus na sakataren a Bauchi?
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadimin gwamnan jihar, Mukhtar Gidado ya wallafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai duk rade-radin cewa Kashim zai tsaya takarar gwamna, babu wata sanarwa a hukumance da ke tabbatar da sha’awarsa na neman kujerar gwamnan.
A 2023, ya samu tikitin takarar gwamna na jam’iyyar PDP, amma daga baya ya janye wanda hakan ya tilastawa jam’iyyar sake gudanar da zaben fidda gwani.
A yayin zaben, Gwamna Bala Mohammed ya yi nasara ba tare da hamayya ba don sake tsayawa takarar gwamna.
Gidado ya ce an umarci shugaban ma’aikatan fadar gwamnati, Aminu Gamawa ya karbi ragamar jagorancin ofishin na rikon kwarya.
Bauchi: Gwamna Bala Mohammed ya yi magana
“Gwamna Bala Mohammed a madadin gwamnati da al’ummar jihar Bauchi ya godewa Ibrahim Kashim kan irin ayyukan da ya yiwa jihar."
Bayan godiya gare shi, gwamnan ya yi masa fatan alheri a rayuwarsa ta gaba,”
Mukhtar Gidado
Abba ya kori sakataren gwamnati a Kano
An ji cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sauke Sakataren Gwamnati (SSG) da kuma rusa ofishin Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnati (COS).
Rahotanni sun nuna cewa gwamnan ya yi sauye-sauyen ma’aikatu tare da sake nada wasu kwamishinoni a ma’aikatu daban-daban.
An sauke wasu kwamishinoni guda biyar daga mukamansu tare da umarnin su gabatar da kansu a ofishin gwamna.
Asali: Legit.ng