2027: Ƙungiyar Ƙabilar Igbo Ta Raba Gari da Atiku kan Kalamansa, Ta Yabawa Tinubu
- Kungiyar kabilar Igbo (Ohanaeze Ndigbo) ta nuna damuwa kan kalaman tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar
- Ta ce abin takaici ne yadda Atiku ya goyi bayan takarar dan Arewa a zaben 2027 wanda hakan ke nuna rashin damuwarsa ga Kudancin kasar
- Ohanaeze Ndigbo ta ce dalilin kalaman nasa, Atiku ya rasa goyon bayan kabilar Igbo da suka dade suna tare da shi idan ya fito takara
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Kungiyar kabilar Igbo (Ohanaeze Ndigbo) ta caccaki tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar.
Kungiyar ta bayyana cewa Atiku ya rasa dukkan goyon baya da kabilar Igbo ke ba shi bayan goyon bayansa ga mulkin 'dan Arewa a zaben 2027.
Ohaenaze Ndigbo ta soki Atiku kan zaben 2027
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakatare-janar na tsagin kungiyar, Okechukwu Isiguzoro ya fitar a Abakaliki, cewar The Guardian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Isiguzoro ya ce kalaman Atiku sun kara tsananta alakar siyasa musamman a tsakanin kabilar Igbo kan yiwuwar take ka’idar karba-karba na shugabancin kasa.
Ya zargi Atiku da kokarin kakkabe sha’awar kabilar Igbo wajen samun wakilci a siyasar Najeriya.
Har ila yau, Isiguzoro ya ce irin wannan dabi’a ta rage martabar Atiku a idanun al’ummar Igbo.
A cewar Ohanaeze, kalaman Atiku sun nuna wata manufa ta ware yankin Kudu daga takarar shugabancin kasa, musamman Peter Obi.
Ƙungiyar ta yabawa Bola Tinubu kan mulkinsa
Kungiyar Ohanaeze ta jaddada cewa ba za ta yarda da wata dabarar siyasa da za ta mayar da al’ummar Igbo baya ko rage musu matsayi a harkokin kasa ba.
Ta yabawa shugaban kasa, Bola Tinubu kan kokarinsa na inganta cigaban ayyukan raya kasa a yankin Kudu maso Gabas.
Isiguzoro ya ce gwamnatin Muhammadu Buhari ta yi shekaru takwas daga 2015 zuwa 2023, ta kuma ba yankin Kudu dama daga 2023 zuwa 2031.
Wani dan PDP ya zanta da Legit Hausa
Kwamred Abdulkadir Abubakar ya ce a siyasa ko mutum biyar ne suka barka asara ce kwarai.
"Sai dai yankin ba Atiku Abubakar suka yi ba a 2023 kowa ya sani, a baya kam an dama da su."
"Duk da haka ba za so hakan ta faru ba amma yanzu ana hasashen haɗaka mai ƙarfi domin samun nasara a 2027."
- Abubakar Abdulkadir
Ya shawarci yan yankin da su mayar da wukarsu musamman idan Atiku da Peter Obi suka hada tafiya.
Atiku na haɗaka da Obi kan siyasar 2027
Kun ji cewa yan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar da Peter Obi na nazarin darasin zaben 2023 da ya gudana a baya saboda shirin siyasa.
Rahotanni sun tabbatar da cewa Atiku da Obi suna duba yiwuwar shiri mai karfi domin tunkarar Bola Tinubu a zaben 2027.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng