'Bai Iya Sata ba ne': APC Ta Kare Gwamna da Ya Gagara Yin Lissafin Kasafin Kudi

'Bai Iya Sata ba ne': APC Ta Kare Gwamna da Ya Gagara Yin Lissafin Kasafin Kudi

  • Bayan tangarda da ba da kunya da gwamnan Edo ya yi yayin gabatar da kasafin kudi, jam'iyyar APC ta kare shi
  • Shugaban APC na reshen jihar Edo, Jarrett Tenebe ya ce abin da Gwamna Monday Okpebholo ya yi ba laifi ba ne
  • Tenebe ya ce hakan shi ke tabbatar da Okpebholo mutum ne mai gaskiya da rikon amana kuma bai iya sata ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Edo - Jam'iyyar APC a jihar Edo ta kare Gwamna Monday Okpebholo kan rikicewarsa yayin mika kasafin kudi a gaban Majalisa.

Shugaban jam'iyyar a Edo, Jarrett Tenebe ya kare Gwamna Okpebholo yayin da tangarda ta faru lokacin gabatar da kasafin kudin shekarar 2025.

APC ta kare gwamna bayan gagara lissafin kasafin kudi
APC a jihar Edo ta kare Gwamna Monday Okpebholo kan gafara furta adadin kasafin kudi. Hoto: Sen. Monday Okpebholo.
Asali: Facebook

Gwamnan Edo ya gagara lissafin kasafin kudi

Vanguard ta ruwaito Tenebe na cewa matsalar da aka samu ya nuna gwamnan bai iya satar kudin al'umma ba.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Dirama yayin da gwamna ya kakare, ya gaza furta adadin kasafin kudi a Majalisa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan ya biyo bayan tangarda da Gwamna Okpebholo ya yi inda ya yi ta fama da kokarin bayyana adadin kudin kasafin N605bn.

“Kasafin kudin jihar Edo na biliyan shida... biliyan 605... miliyan 76...”

Cewar gwamnan yayin da muryarsa ke rawa, bayan gwadawa sau da dama ba tare da nasara ba, Okpebholo ya ce:

“Ku yi hakuri, abin yana rikitar da ni ne."

Wannan maganar ta jawo abin dariya da ƙananan maganganu a cikin zauren Majalisar, cewar Punch.

Jam'iyyar APC ta kare gwamna bayan katobara

A martaninsa, Tenebe ya kare gwamnan inda ya danganta matsalar wajen lissafin kudade da gaskiyar Okpebholo da rashin aikata cin hanci.

“Kafafen yada labarai sun cika da surutun da ake yi kan gwamnan game da kasafin kudin N605bn da sauran abubuwan da suka biyo baya,”
"Abu ne na al’ada, kowa na iya yin irin wannan kuskuren, ni ma ban san lissafi ba, kuma haka ake gane mutum mai gaskiya da rikon amana."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi ɓarin wuta a cikin gari, sun yi garkuwa da hadimin tsohon gwamna

"Monday Okpebholo ba mai laifi ba ne, bai kuma saba da lissafi ba, duk wanda zai yi magana, ya ci gaba, kawai yana magana ne barkatai.”

- Jarrett Tenebe

An daure dan takarar gwamna a gidan kaso

Kun ji cewa wata kotun majistare a jihar Edo ta daure wani dan siyasa mai suna Paul Okungbowa kan zargin bata suna da cin zarafi.

Kotun ta daure Okungbowa wanda ya yi takara a zaɓen gwamnan Edo da aka gudanar a 2024 karkashin jam'iyyar YPP.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.