Shirin Kayar da Tinubu: APC Ta Fadi Abin da Zai Faru da Atiku, Obi a Zaben 2027
- APC ta bayyana cewa haɗin gwiwa tsakanin Atiku Abubakar da Peter Obi ba zai iya hana Bola Tinubu sake lashe zabe a 2027 ba
- Bala Ibrahim, mai magana da yawun APC ya ce jam’iyyun adawa suna fama da rikici, kuma hakan zai hana su yin tasiri mai karfi
- APC ta ce ta kafa cibiyar 'Progressive Institute' domin ba da horo kan adawa, inda ta ce 'yan adawa za su koyi sabon darasi a 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Jam’iyyar APC ta bugi kirji tare da ikirarin cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da Peter Obi ba za su kai labari a 2027 ba.
APC ta yi gargadin cewa babu wani kawance tsakanin shugabannin adawa, irin su Atiku da Obi, da zai hana Shugaba Bola Tinubu sake cin zabe a 2027.
Bala Ibrahim, daraktan yada labarai na APC, ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da jaridar The Punch a ranar Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan adawa na shirin kayar da Tinubu
Mista Ibrahim ya mayar da martani kan kalaman Paul Ibe, mai magana da yawun Atiku, na cewa Atiku da Obi za su hade domin hambarar da gwamnatin APC.
Paul Ibe ya ce kuri’un Atiku da Obi da suka kai miliyan 12 a zaben da ya gabata za su iya hana Tinubu sake samun mulki.
Shi ma mai magana da yawun Obi, Umar Ibrahim, ya ce Obi zai yi hadaka da duk dan siyasar da suke da ra'ayi daya, da nufin ciyar da Najeriya gaba.
APC ta gargadi shugabannin adawa
Sai dai Bala Ibrahim ya bayyana haɗin gwiwar Atiku da Obi a matsayin wani mafarki mara tabbaci, yana cewa hakan ba zai yi tasiri ba.
Ya kara da cewa jam’iyyun adawa suna fama da rikice-rikice da za su hana su yin takarar da za ta iya yin tasiri a zaben 2027.
"Idan hadakar ce burinsu, to tun yanzu za mu shirya bikin nasara a 2027 saboda APC za ta sake doke su da tazara mai yawa."
- A cewar daraktan yada labaran.
Bala Ibrahim ya ce jam’iyyar APC ta bude makaranta 'Progressive Institute' domin 'yan adawa su zo da litattafai da biro su koyi darasi kan adawa mai amfani.
An fadi kuskuren Atiku, Obi a 2023
A wani labarin, mun ruwaito cewa Ismael Ahmed, wani kusa a jam'iyyar APC reshen jihar Kano ya ce Atiku Abubakar da Peter Obi ne suka jawo nasarar APC a 2027.
Ismael Ahmed ya yi nuni da cewa da yanzu Bola Ahmed Tinubu ba shi ne shugaban Najeriya ba da ace Atiku da Obi sun hada kai a zaben 2023 da ya gabata.
Asali: Legit.ng