Uwar Bari: Lauya Ta ba Bello El Rufai Hakuri da Ya Yi Barazanar Maka Ta a Kotu kan Kazafi

Uwar Bari: Lauya Ta ba Bello El Rufai Hakuri da Ya Yi Barazanar Maka Ta a Kotu kan Kazafi

  • Dan Majalisar Tarayya daga jihar Kaduna, Bello El-Rufai ya yi barazanar maka wata lauya a kotu bayan ta wallafa rubutun karya kansa
  • Lauyar mai suna Sabina Nkiru Ezeoke ta nemi afuwa kan zargin da ta yi wa Bello El-Rufai inda ta ce ta yi nadamar abin da ta yi
  • Hakan ya biyo bayan zargin cewa hukumar EFCC ta kai samame gidan dan Majalisar. aka kara da cewa ta samu muggan kwayoyi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna - Wata lauya a Najeriya mai suna Sabina Nkiru Ezeoke ta nemi afuwar Hon. Bello El-Rufai kan kazafi.

Lafiyar ya nemi afuwar kan wasu zarge-zarge da ta yi wa dan Majalisar Tarayya da ke wakiltar Kaduna ta Arewa.

Lauya ta nemi yafiyar Bello El-Rufai kan bata masa suna
Lauya a Najeriya ta roki Bello El-Rufai ya yafe mata kan kazafin da ta yi masa. Hoto: Bello El-Rufai.
Asali: Twitter

Lauya ta yi wa Hon. Bello El-Rufai kazafi

Kara karanta wannan

Majalisa ta fahimci halin da ake ciki, ta taso bankin CBN a gaba kan takardun kuɗi

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da dan Majalisar ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan na zuwa ne bayan lauyar ta yi rubutu a kafar sadarwa inda take zargin an kai samame gidan Bello El-Rufai.

Lauyar ta ce yayin samamen an gano muggan kwayoyi a gidan dan Majalisar na miliyoyin naira a Kaduna, ta yi ikirarin cewa an gano $800bn da N700bn da miyagun kwayoyi na N1trn.

Bello El-Rufai ya musanta rade-radin da ake yaɗawa

Bello ai El-Rufai ya musanta wannan batu, ya ce labarin karya ne da ake amfani da shi don juyar da tunanin al'umma da haddasa rikici.

Ya ce yunƙurin da ake yi na danganta shi da ayyukan da ba su dace ba ta hanyar zarge-zarge marasa tushe ba kawai cin mutuncinsa ba ne, har ma da cin zarafin adalci da gaskiya.

Bayan gano cewa labarin ba gaskiya ba ne, Nkiru ta janye maganarta, ta ce ba ta tantance sahihancin bayanan ba kafin ta wallafa su ta ce duk wani ƙoƙarinta domin ganin ta tantance labarin kafin wallafawa ya ci tura.

Kara karanta wannan

Tsohon mai ba Jonathan shawara ya fadi abin da zai faru da tattalin Najeriya kwanan nan

"Na gano cewa wannan bayani ba gaskiya ba ne kwata-kwata, domin haka ina roƙonka ka karɓi wannan takarda a matsayin janye maganata da kuma neman afuwa na da gaske."
"Ba ni da wata niyyar cin mutunci ko kunyata ka, iyalanka, ko Majalisar Wakilai ta Tarayya ko kuma ɓata sunanka."

- Sabina Nkiru Ezeoke

Bello El-Rufai ya gana da Adams Oshiomhole

Kun ji cewa Honarabul Bello El-Rufai ya hadu da Adams Oshiomhole wanda yake tsananin girmamawa kamar ubansa.

Kafin tsohon shugaban na APC ya zama Sanata, Hon. Bello El-Rufai ya yi aiki a matsayin babban hadimin Uba Sani.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.