Ado Doguwa: 'Dan Majalisa Ya Nemi Afuwar APC kan Yabon Gwamnan PDP

Ado Doguwa: 'Dan Majalisa Ya Nemi Afuwar APC kan Yabon Gwamnan PDP

  • Ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Doguwa/Tudunwada daga Kano, ya nemi afuwar jam'iyyar APC ta reshen jihar Osun
  • Alhassan Ado Doguwa ya bayyana cewa PDP ce ta sauya kalamansa domin cimma wata manufa ta siyasa domin harzuƙa APC
  • Ɗan majalisar ya nuna cewa bai yi kalaman domin kunyata APC ba kuma da yardar Allah za ta dawo kan mulkin jihar a 2026

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ɗan majalisar wakilai, Alhassan Ado-Doguwa, ya nemi afuwar jam’iyyar APC reshen jihar Osun.

Hon. Alhassan Ado Doguwa ya nemi afuwar ne bisa kalaman da ya yi a wajen bikin ranar Ede na shekarar 2024.

Doguwa ya nemi afuwar APC
Ado Doguwa ya nemi afuwa wajen APC reshen jihar Osun Hoto: Alhassan Ado Doguwa
Asali: Twitter

Ɗan majalisar ya nemi afuwar ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, 10 ga watan Disamban 2024, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

An yi musayar yawu da wani ɗan Majalisar Tarayya ya sanar da komawa APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Neman afuwar ta sa na zuwa ne bayan jam'iyyar APC reshen jihar Osun, ta zarge shi da ƙoƙarin ɓata mata suna bayan ya yabi Gwamna Ademola Adeleke na PDP, rahoton Leadership ya tabbatar.

Ado Doguwa ya nemi afuwar jam'iyyar APC

Sai dai, Doguwa ya bayyana cewa da gangan jam'iyyar PDP ta yi amfani da kalaman nasa domin cimma wata manufa ta siyasa.

"Jam'iyyar PDP a jihar Osun ta sauya kalamaina domin cimma wata manufa ta siyasa. Wannan wani yunƙuri ne da gangan domin cimma muradun siyasa."
"Ina son neman afuwar ƴan uwanmu na APC a jihar Osun. Da fatan za ku yi mano uzuri. Da yardar Allah kwanakin PDP a jihar Osun sun kusa zuwa ƙarshe.
"A shekarar 2026, jam'iyyarmu za ta farfaɗo a jihar Insha Allah."
"Na kasance babban mai tallata jam’iyyar APC a faɗin ƙasar nan har da jihar Osun."
"Ban taɓa nufin na kunyata ko kushe jam'iyyarmu ta kowace hanya ba."

Kara karanta wannan

"Ban saɓawa Doka ba," Ƴar Majalisar Tarayya ta faɗi dalilinta na fita daga PDP zuwa APC

- Alhassan Ado Doguwa

Kotu ta yi hukunci kan shari'ar Doguwa

A wani labarin kuma, kun ji cewa kotun ɗaukaka ƙara ta zartar da hukunci kan zargin kisan kai da ake yi wa Hon. Alhassan Ado Doguwa a lokacin zaɓen 2023.

Kotun ɗaukaka ƙarar a tabbatar da wanke ɗan majalisar wakilan mai wakiltar Doguwa/Tudunwada, sannan ta haramtawa Gwamna Abba Kabir kama shi da kuma cin zarafinsa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng