Jigo a NNPP Ya Yi Martani kan Bukatar 'Yan Arewa Su Hakura da Karawa da Tinubu a 2027

Jigo a NNPP Ya Yi Martani kan Bukatar 'Yan Arewa Su Hakura da Karawa da Tinubu a 2027

  • Wani ƙusa a jam'iyyar NNPP, Buba Galadima, bai ji daɗin kalaman sakataren gwamnatin tarayya kan zaɓen shekarar 2027 ba
  • Buba Galadima ya bayyana kalaman George Akume na buƙatar ƴan Arewa su haƙura da neman shugaban ƙasa a 2027, a matsayin abin dariya
  • Jigon na NNPP ya nuna cewa zaɓen wanda zai jagoranci ragamar ƙasar nan, ya rataya nw a kan wuyan ƴan Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Jigo a jam'iyyar NNPP, Buba Galadima, ya bayyana kalaman sakataren gwamnatin tarayya, George Akume, a matsayin abin dariya.

George Akume dai ya nemi ƴan arewa masu burin yin takarar shugaban ƙasa da su jira har sai 2031, lokacin da Bola Tinubu zai kammala wa'adinsa na biyu.

Buba Galadima ya yi magana kan zaben 2027
Buba Galadima ya yi wa George Akume martani Hoto: Buba Galadima
Asali: Facebook

Buba Galadima ya yi wa George Akume martani ne, yayin wata tattaunawa da tashar Arise News.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Atiku ya maida martani bayan Akume ya bukaci ya hakura da takara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane martani Buba Galadima ya yi?

Buba Galadima ya bayyana cewa yadda mutane ke ji yanzu a jikinsu, shi ne zai tabbatar da yadda za su kaɗa ƙuri'a a zaɓen 2027.

"Ba zan tattauna batutuwan Najeriya kan batun Arewa da Ƙudu ba. Ni ɗan kishin ƙasa ne."
"Abin da mutane ke ji yanzu a jikinsu, shi ne zai tabbatar da yadda za su kaɗa ƙuri’a a 2027."
"Akwai babban gurbi, a haƙiƙanin gaskiya babu wanda ya hau wannan kujera a 2027 kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada. Domin haka, kalaman Akume abin dariya ne kawai."
"Babu wata barazana da wani zai yi, babu wani kisa da wani zai yi wanda zai hana ƴan Najeriya samar da ɗan takarar da zai nemi kujerar."
"A yanzu mun san cewa wannan gwamnatin ta APC tana tura wakilai domin shawo kan shugabannin jam'iyyu, inda suke musu tayin maƙudan kuɗaɗe."
"Suna son dukkanin jam'iyyaun siyasa su yarda da manufofin wannan gwamnatin, ta yadda a 2027 ba za a samu wani ɗan takara ba."

Kara karanta wannan

'Dan takarar shugaban kasa ya yabi Tinubu ana batun kudirin haraji

- Buba Galadima

PDP ta hango faɗuwar Tinubu a 2027

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta taya mutanen ƙasar Ghana murnar zaɓen sabon shugaban ƙasan da suka yi.

Jam'iyyar PDP ta bayyana cewa nasarar ƴan adawa a ƙasar Ghana babbar alama ce da ke nuna ƙarshen mulkin Bola Tinubu da APC ya zo ƙarshe a Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng