APC Ta Kassara PDP a Zamfara, Dan Majalisar Tarayya Ya Karbi Mutane 1,500
- Jam'iyyar APC ta yi wa Gwamna Dauda Lawal Dare illa a jihar Zamfara bayan karbar masu sauya sheka daga adawa
- Hon. Aminu Sani Jaji shi ya karbi sababbin tuban zuwa APC da suka kai mutane 1,500 daga jam'iyyu daban-daban
- Jam’iyyun da mambobin nasu da suka koma APC sun hada da PDP da APGA da YPP da wasu ƙananan jam’iyyu
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Zamfara - Dan Majalisar Wakilai, Aminu Jaji daga jihar Zamfara ya karɓi mutane 1,500 da suka sauya sheƙa zuwa APC
Hon. Aminu Jaji da ke wakiltar Mazabar Birnin Magaji/Kaura Namoda, ya karɓi mutane 1,500 da suka sauya sheƙa daga jam’iyyun PDP da APGA da YPP da wasu ƙananan jam’iyyu.

Source: Facebook
Hon. Aminu Jaji ya karbi yan adawa a Zamfara
Wannan na kunshe a cikin wata sanarwa da hadimin Hon. Jaji kan bangaren yada labarai, Jamilu Iliyasu ya fitar a Gusau, cewar PM News.
Ilyasu ya bayyana cewa waɗanda suka sauya sheƙar sun haɗa da shugabanni da magoya bayan jam'iyyar PDP da APGA da YPP da sauran jam’iyyu a fadin jihar.
Ya ce matakin abu ne mai kyau ga jam’iyyar APC tare da tabbatar musu da adalci da kyakkyawar dangantaka domin ƙarawa jam’iyyar ƙarfi a jihar.
A yayin taron, Hon. Aminu Jaji wanda ya samu wakilcin shugaban kungiyar Jajiyya, Alhaji Isiyaka Ajiya-Anka ya yabawa wadanda suka sauya shekar.
Zamfara: Dubban 'yan PDP da suka koma APC
A cewar Iliyasu, fitattun ‘yan siyasa da suka sauya sheƙar sun haɗa da tsohon Shugaban APGA a jihar, Alhaji Rabi’u Salisu-Bature da ɗaruruwan mambobinta, Daily Post ta ruwaito.
Haka zalika, akwai Shugaban YPP na Zamfara, Alhaji Sani Anka da ɗaruruwan mambobin YPP daga sassa daban-daban na jihar.
Sauran sun haɗa da jagoran PDP daga karamar hukumar Shinkafi da tsohon darakta-janar, Alhaji Nasiru Yusuf da tsohon dattijo kuma jigo a PDP, Malam Ibrahim Tado.
Rikicin APC ya yi kamari a Adamawa
Kun ji cewa jam’iyyar APC mai adawa ta kafa kwamitin sulhu mai mutum takwas domin daidaita rikice-rikicen cikin gida a jihar Adamawa.
An bayyana kwamitin ne yayin wani taro a Yola karkashin jagorancin mataimakin shugaban APC na Arewa maso Gabas, Mustapha Salihu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng

