APC Ta Dura kan Atiku a kan Jifanta da Amfani da Wike wajen Hura Wuta a Jam'iyyar PDP
- Kakakin Atiku Abubakar ya zargi APC da amfani da ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike wajen ruguza PDP
- Biyo bayan zargin, jam'iyyar APC ta musanta lamarin, tana mai cewa PDP ce ke da matsalar cikin gida
- APC ta bayyana cewa Nyesom Wike ba dan jam’iyyar ta ba ne, kuma ba ta aiki tare domin cimma muradunta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Jam’iyyar PDP ta sake sababbin zarge-zarge game da matsalolin cikin gida da ta ke fama da su tun kafin zaben 2023.
Yayin da rikicin PDP ya yi kamari, kakakin tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya zargi APC da amfani ministan Abuja, Nyesom Wike domin lalata PDP.

Source: Facebook
Punch ta wallafa cewa daraktan yada labaran APC ne ya yi martani bayan zargin da Paul Ibe ya yi a ranar Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Pail Ibe ya yi zargin cewa APC tana amfani da rikicin PDP domin kara dagula lamarin, har ma tana kai rikicin zuwa ga sauran jam’iyyun adawa.
Rikicin PDP: APC ta yi martani ga Atiku
Jam’iyyar APC ta maida martani ga Atiku cikin hanzari ta hannun babban daraktan yada labaranta, Bala Ibrahim, wanda ya musanta wannan zargi.
Bala Ibrahim ya ce babu wata hujja da ke nuna cewa Wike yana aiki da APC domin ruguza PDP, musamman ganin cewa Wike har yanzu ba dan jam’iyyar APC ba ne.
Daraktan yada labaran ya ce Wike ba 'dan APC ba ne kuma bai taba bayyana cewa yana bin umarnin APC ba.
Rikicin jam'iyya: APC ta ba PDP shawara
Bala Ibrahim ya ce lokaci ya yi da PDP za ta fuskanci matsalolinta da gaske, maimakon ta ci gaba da zargin wasu da yin katsalandan a harkokinta.

Kara karanta wannan
An ajiye Atiku, Kwankwaso: An fadi mutum 1 da zai iya kwace mulki a hannun Tinubu
Bugu da kari, Bala Ibrahim bayyana cewa APC tana da matsaloli da dama da ta ke mayar da hankali kansu fiye da shiga rikicin PDP.
Cacar bakin na zuwa ne a lokacin da PDP ke kokarin sake dawo da martabarta a fagen siyasa bayan faduwa a zaben shugaban kasa na 2023.
Jam'iyyar PDP ta yi magana kan Wike
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban PDP ya yi tsokaci kan lamarin Nyesom Wike da korafe-korafen da ake yi a kansa bayan karbar mukamin minista.
Rahotanni sun nuna cewa tun bayan rasa takarar shugaban kasa a 2023 ,Wike ya fara nuna alamun rashin shiga tafiyar jam'iyyar PDP dari bisa dari.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng
