Zaben 2027: Abin da Atiku da Obi Ke Shiryawa Tinubu bayan Yin Kura Kurai a 2023
- 'Yan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar da Peter Obi na nazarin darasin zaben 2023 da ya gudana a baya saboda shirin zaben 2027
- Rahotanni sun tabbatar da cewa Atiku da Obi suna duba yiwuwar shiri mai karfi domin tunkarar Bola Tinubu a takarar shugaban kasa
- Hakan ya biyo bayan rade-radin cewa yan adawa na kokarin yin hadaka mai karfi domin kifar da Tinubu, a hana shi zarcewa a mulki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Rahotanni sun tabbatar da cewa Atiku Abubakar da Peter Obi suna wani shiri na musamman kan zaben 2027.
An tabbatar da cewa 'yan takarar shugaban kasa, Atiku da Peter Obi suna duba kura-kuran da suka tafka a zaben 2023.
Shirin Atiku da Peter Obi kan zaben 2027
Mai magana da yawun Atiku Abubakar mai suna Paul Ibe ya bayyana hakan a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ibe ya ce Atiku Abubakar tare da dan takarar LP, Peter Obi sun bayyana cewa suna nazarin darasin da suka koya daga zaben 2023 da ya gabata.
Ya ce sun fahimci muhimmancin hadin kai tsakanin ‘yan adawa kuma suna tattaunawa kan yadda za a kaucewa maimaita kura-kuran baya.
“Tattaunawa na gudana tsakanin manyan jiga-jigan siyasa domin tabbatar da cewa ba a sake maimaita irin kura-kuran baya ba,”
- Paul Ibe
'Obi bai yi wa Atiku illa a 2023 ba' - Ibe
Haka kuma, Ibe ya karyata ikirarin da ke cewa ficewar Peter Obi daga jam’iyyar PDP ce ta kawo cikas ga nasarar Atiku a zaben 2023.
Ibe ya bayyana haka yayin martani kan kalaman Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), George Akume.
Atiku Abubakar ya yi wa Akume raddi
Akume ya bukaci ‘yan siyasar Arewacin Najeriya da su bari Shugaba Bola Tinubu ya yi wa’adi biyu har zuwa 2031, cewar Daily Post.
Sai dai Ibe ya ce ba hakkin Akume ba ne ya danne muradin duk wanda ke da ikon takarar shugabancin kasa.
Ya yi kira ga jam’iyyar APC da ta bari kowa ya samu ‘yancin yin siyasa, ya ce wajibi ne a bar filin siyasa a bude ga kowa ba tare da tauye hakkin kowa ba.
2027: Yadda Atiku, Obi za su kada Tinubu
Kun ji cewa yayin da jam'iyyun adawa suka fara shirin zaɓen 2027, ana ganin ya zama tilas Atiku Abubakar da Peter Obi su ɗinke ɓarakar da ke tsakaninsu.
Hadimin Atiku, Paul Ibe ya ce mai gidansa da Obi suna gagarumin shiri a zaɓen shugaban ƙasa na 2027 kuma za su haɗa kai domin karya jam'iyyar APC.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng