'Abin da Ya Kamata Atiku da Peter Obi Su Yi don Kayar da APC a Zaben 2027'
- Paul Ibe ya ce Atiku Abubakar da Peter Obi sun gane kuskurensu, kuma sun shirya haɗewa wuri ɗaya domin karya APC
- Hadimin tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce maigidansa ya fara tuntuɓar ƴan adawa domin su haɗa kai su yi aiki tare
- Ya ce haɗuwar Atiku Obi ce kaɗai hanyar da ta rage idan ana son kawo ƙarshem gwamnatin APC a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Yayin da jam'iyyun adawa suka fara shirin babban zaɓen 2027, ana ganin ya zama tilas Atiku Abubakar da Peter Obi su ɗinke ɓarakar da ke tsakaninsu.
Babban jigon PDP, Paul Ibe ya ce Atiku Abubakar da Peter Obi sun ɗauki darasi a zaɓen shugaban ƙasa na 2023 kuma za su haɗa kai domin karya APC.
Mista Paul Ibe, mai magana da yawun Atiku na PDP ya yi wannan furucin ne shirin siyasa a yau na Channels tv yau Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda Atiku da Obi suka rasa dama a 2023
Atiku da Obi na jam’iyyar LP, kowanensu ya samu kuri’u sama da miliyan shida a zaben shugaban kasa na 2023 wanda Bola Tinubu na APC ya lashe.
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya ci zaɓen ne da ƙuri'u miliyan takwas, wanda ke nuna da Atiku da Obi na tare wataƙila da sun kai labari.
Masu fashin baki dai sun ce jam'iyyar PDP ta zubar da damarta na kwace mulki daga hannun APC mai-ci ta hanyar raba kuri'u da jam'iyyar LP.
Atiku da Peter Obi sun gane kuskurensu
Da yake tsokaci kan hakan, Paul Ibe ya ce manyan ƴan adawar guda biyu watau Atiku da Obi sun ɗauki darasi kuma ba za su maimaita kuskuren da suka yi a 2023 ba.
Hadimin tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi tsokaci kan ganawar Atiku da Obi, inda ya ce wannan wani sabon salo ne a siyasa.
Paul Ibe ya ce:
"A zahirin gaskiya Atiku ya tuntuɓi jam'iyyun adawa domin su yi aiki tare, ta haka ne kaɗai za su iya karya wannan gwamnatin ta mayaudara, yanzu haka ana ci gaba da tattaunawa."
Jigon APC ya tono kuskuren Atiku, Obi
A wani rahoton, an ji cewa wani ƙusa a jam'iyyar APC a jihar Kano ya taɓo batun nasarar da shugaba Bola Tinubu ya samu a zaɓen 2023
Ismael Ahmed ya bayyana cewa da a ce ƴan adawa, Atiku Abubakar da Peter Obi, sun haɗa kai, da Tinubu bai kai labari ba a zaɓen shugaban ƙasa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng