"Ban Saɓawa Doka ba," Ƴar Majalisar Tarayya Ta Faɗi Dalilinta na Fita daga PDP zuwa APC
- Ɗiyar tsohon gwamnan jihar Delta da ke majalisar wakilai ta ƙalubalanci matakin PDP na ayyana kujerarta da babu kowa
- Hon. Erhiatake Ibori-Suenu ta shaidawa babbar kotun tarayya da ke Abuja dalilinta na barin PDP, inda ta ce ba ta saɓawa tanadin kundin tsarin mulki ba
- Ƴar Majalisar ta sanar da sauya sheka daga PDP zuwa APC a zauren Majalisa ranar Alhamis, lamarin da ya harzuƙa babbar jam'iyyar adawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Delta - Ƴar Majalisar wakilan tarayya, Hon. Erhiatake Ibori-Suenu ta jaddada cewa sauya shekar da ta yi zuwa APC ba ta saɓawa tanadin kundin tsarin mulki ba.
Ibori-Suenu, ɗiyar tsohon gwamnan Delta, James Ibori ta ce matakin da ta ɗauka yana kan doka, don haka ba dalilin da PDP za ta ayyana kujerarta da babu kowa.
'Yar Majalisa ta faɗi dalilin komawa APC
Vanguard ta tattaro cewa ƴar majalisar ta yi wannan bayani ne a takardar ƙorafin da ta kai kotu, inda ta sake zayyana dalilinta na ficewa daga PDP zuwa APC.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Idan baku manta ba ɗiyar tsohon gwamnan ta samu nasarar lashe zaɓen mamba mai wakiltar mazaɓar Ethiope ta Gabas/Yamma a Majalisar wakilai a zaɓen 2023.
Ta samu nasara ne a inuwar jam'iyyar PDP duk a lokacin mahaifinta, James Ibori ya samu saɓanin siyasa da gwamnan Delta mai ci a lokacin, Ifeanyi Okowa.
PDP ta yi fatali da sauya sheƙarta
A ranar Alhamis da ta gabata, Hon. Ibori-Suenu ta sanar da komawa APC a hukumance a wata wasiƙa da ta miƙawa shugaban Majalisar, Rt. Hon. Tajudeen Abbas.
Sai dai jam'iyyar PDP ta bayyana cewa ƴar majalisar ta rasa kujerarta tun da ta zaɓi komawa APC.
A takardar da ta shigar a babbar kotun tarayya kan sauya shekar, ƴar Majalisar ta sanya shugaban Majalisar, magatakarda da jam'iyyar PDP a matsayin waɗanda take ƙara.
Diyar Ibori ta kare kanta a kotu
Ibori-Suenu ta ce rigingimun cikin gida ne dalilinta na barin wanda ake tuhuma na 3 watau jam'iyyar PDP.
"Sama da shekara guda PDP na fama da rigingimu wanda har ta kai ga jam'iyyar ta dare gida biyu," in ji ta.
Majalisa na neman rage ministoci zuwa 37
A wani rahoton kun ji cewa Majalisar wakilai ta hannun kwamitin da ta kafa kan gyaran kundin tsarin mulkin Najeriya ta gabatar da bukatar rage ministoci zuwa 37.
Ƴan majalisar sun bayyana cewa idan aka kayyade yana ministocin, za a rage kashe kuɗaɗe a bangaren majalisar zartarwa.
Asali: Legit.ng