"Da Tinubu Ya Fadi": Kusa a APC Ya Fadi Kuskuren Atiku da Peter Obi a 2023
- Wani ƙusa a jam'iyyar APC a jihar Kano ya taɓo batun nasarar da Shugaba Bola Tinubu ya samu a zaɓen 2023
- Ismael Ahmed ya bayyana cewa da ace ƴan adawa, Atiku Abubakar da Peter Obi, sun haɗa kai, da Tinubu bai kai labari ba a zaɓen shugaban ƙasa na 2023
- Jigon na APC ya nuna cewa ba ya fatan Atiku da Peter Obi su yi haɗaka a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027 da ake tunkara
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Wani jigon jam'iyyar APC a jihar Kano, Ismael Ahmed, ya yi magana kan nasarar da Shugaba Bola Tinubu ya samu a zaɓen 2023.
Jigon na APC ya ce da ace Atiku Abubakar da Peter Obi sun haɗa kai a 2023, da Shugaba Bola Tinubu bai yi nasara ba.

Source: Facebook
Ismael Ahmed ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa a shirin 'Mic on Podcast'.
Me jigon APC ya ce kan haɗakar Atiku da Obi
Jigon na APC ya bayyana cewa ka da Allah ya sanya jagororin na ƴan adawa su yi haɗaka a zaɓen 2027.
Da aka tambaye shi ko ya damu kan yiwuwar yin haɗakar Atiku da Peter Obi, sai ya ka da baki ya ce:
"Eh gaskiya na yi. Ɓan taɓa ɗaukar duk wata barazana a siyasa a matsayin wasa ba. Sannan idan ka kalli ƙuri'un Atiku da na Obi a 2023, da mun faɗi zaɓe idan aka haɗa su waje ɗaya. Allah ya kiyaye su yi haɗaka."
- Ismael Ahmed
Atiku da Peter Obi sun sake dawo da batun yiwuwar yin haɗakarsu ne bayan an gansu tare a birnin Yola na jihar Adamawa.
Ganawar da suka yi a Yola ta ɗauki hankula kan shirinsu na zaɓen 2027, inda wasu rahotannin ke cewa akwai yiwuwar sun fara duba yiwuwar yin haɗaka.
Peter Obi dai shi ne babban mai jawabi a wajen bikin cika shekara 20 da kafa jami'ar American University of Najeriya (AUN), wacce mallakar Atiku ce.
Atiku da Obi sun musanta batun haɗaka
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, Atiku Abubakar da Peter Obi sun musanta batun shirin yin haɗaka kan zaɓen 2027.
Mutanen biyu sun faɗi hakan ne bayan an fara yaɗa jita-jitar cewa za su haɗe waje ɗaya sakamakon ganinsu tare da aka yi a birnin Yola na jihar Adamawa.
Asali: Legit.ng

