Ana Shirin Koyawa APC Darasi, Ganduje Zai Fuskanci babbar Matsala a Wasu Jihohi 2
- Gwamna Seyi Makinde ya ce akwai 'karancin tunani' a furucin Abdullahi Ganduje na cewa APC za ta kwace jihohin Osun da Oyo
- Gwamnan na jihar Oyo ya ce al'umomin jihohin Osun da Oyo suna jiran APC a zabe mai zuwa domin su koya mata babban darasi
- A yayin kaddamar da wasu ayyuka a Osun, Makinde ya nemi 'yan jihar da su sake zaben Ademola Adeleke domin dorewar cigaba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Osun - Gwamnan Oyo, Seyi Makinde, ya ce lissafi ya kwacewa shugaban APC, Abdullahi Ganduje, da har yake ikirarin cewa zai kwace jihohin Osun da Oyo.
Makinde ya ce Ganduje ya saki layi yayin da ya yi wannan furuci kuma ya yi kuskuren tunanin cewa abin da ya faru a Ondo da Edo zai faru a Osun da Oyo.
Za a koyawa APC darasi a Oyo da Osun
Gwamna Makinde ya ce mutanen Osun za su koyawa APC darasi a zaɓen gwamnoni mai zuwa saboda hazakar Ademola Adeleke, inji rahoton Channels.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Makinde ya yaba wa mutanen Osun kan zaben Adeleke shekaru biyu da suka wuce, inda ya ce hakan ya kawo ci gaba mai yawa a jihar.
Gwamnan ya kuma yaba wa Adeleke bisa cigaba da zartar da ayyukan da ya gada daga tsofaffin gwamnonin jihar da aka gagara karasawa.
An roki 'yan jihar Osun su sake zabar PDP
Ya ce bin manufofi da ayyuka masu amfani ga al’umma shine hanyar magance matsalolin tattalin arziki da suka addabi Najeriya.
Gwamna Makinde ya bukaci masu zabe a Osun su goyi bayan Adeleke domin ya yi tazarce na shekaru hudu bayan kammala wa'adinsa na farko.
Ya yi ikirarin cewa su biyu ne gwamnonin da suka fi kamanta gaskiya da kuma gudanar da ayyuka masu amfani a Kudu maso Yamma.
Ganduje ya ce APC za ta kwace Osun da Oyo
Tun da fari, mun ruwaito cewa shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ya lashi takobin kwace jihohin Osun da Oyo daga hannun jam'iyyar PDP.
Abdullahi Ganduje ya yi wannan furucin ne bayan da APC ta samu nasarar lashe zabukan jihohin Ondo da Edo da hukumar INEC ta gudanar da kwanakin baya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng