PDP Ta Kara Babban Rashi, Ƴar Tsohon Gwamna da ke Majalisa Ta Sauya Sheƙa Zuwa APC
- Ƴar majalisar wakilan tarayya daga jihar Delta, Erhriatake Ibori-Suenu ta fice daga PDP zuwa jam'iyyar APC mai mulki
- Erhriatake Ibori-Suenu, ɗiyar tsohon gwamna, James Ibori ta sanar da haka ne a wasiƙar da ta miƙawa kakakin majalisar wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas
- Ɗiyar tsohon gwamnan ta samu nasara a zaben 2023 duk da rigimar siyasa da ta shiga tsakanin mahaifinta da gwamna mai ci a lokacin, Ifeanyi Okowa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Ƴar majalisar wakilan tarayya mai wakiltar mazaɓar Ethiope a jihar Delta, Erhriatake Ibori-Suenu ta sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC.
Misis Ibori-Suenu, diyar tsohon gwamnan Delta James Ibori, ta sanar da sauya shekarta ne a wata wasika da ta aikewa shugaban majalisar, Rt. Hon. Tajudeen Abbas.
Tajudeen ya karanta wasikar sauya sheƙar a zaman yau Alhamis, 5 ga watan Disamba, 2023, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda ƴar majalisar ta ci zaɓe a 2023
Ƴar majalisar ta samu nasarar lashe zabe a 2023 a karkashin inuwar jam'iyyar PDP duk da sabanin siyasar mahaifinta da tsohon gwamna, Ifeanyi Okowa.
Mista James Ibori, na hannun damar shugaban ƙasa Bola Tinubu, ya samu sabani da Okowa, gwamnan Delta a wancan lokacin kan zaben wanda zai gaje shi.
Tsohon gwamnan wanda ake ganin yana da ƙarfin siyasa a Delta, ya goyi bayan takarar David Edebvie amma Okowa ya zagaye ya marawa Sheriff Oborevwori baya.
A ƙarshe kuma Sheriff Oborevwori ya samu nasarar lashe tikitin takarar gwamna na PDP a zaɓen fidda gwani.
Ɗiyar tsohon gwamnan ta koma APC
A halin yanzu dai ɗiyar tsohon gwamnan, Erhriatake Ibori-Suenu ta tattara kayanta ta fice daga PDP zuwa jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya.
Sai dai bayan sanar da sauya shekar ɗiyar Ibori a zauren majalisa, mai ladabtarwa na marasa rinjaye, Ali Isa ya nemi a ayyana kujerarta a matsayin wanda aka rasa.
Nan take kakakin majalisar, Tajudeen Abbas ya yi fatali da bukatarsa ta hanyar da ya dace, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Ƴan majalisa 4 na LP sun koma APC
A wani rahoton kun ji cewa ƴan majalisar wakilai huɗu sun tattara sun bar jam'iyyar LP zuwa APC mai mulki ranar Alhamis.
Ɗaya daga cikin masi sauya shekar wanda ya fito daga jihar Kaduna, Hon. Donatus Matthew, ya ce sun ɗauki matakin barin LP ne saboda rikicin da ya ƙi ƙarewa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng