Kwamitin Amintattu na PDP Ya Fara Bin Hanyoyin Warware Rikicin Jam'iyyar
- Kwamitin amintattu na PDP (BoT) ya taso shugabannin jam'iyyar a gaba kan ci gaba da ɗage taron NEC
- Shugaban kwamitin amintattun ya buƙaci shugabannin na PDP da su tabbatar sun gudanar da taron NEC a watan Fabrairun 2025
- Sanata Adolphus Wabara ya kuma bayyana cewa kwamitin BoT zai gana da Nyesom Wike kan rikicin jam'iyyar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP (BoT) ya soki kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC), ƙarƙashin jagorancin Umar Damagum.
Kwamitin amintattun ya caccaki shugabannin na PDP ne kan ci gaba da ɗage taron kwamitin zartaswa na ƙasa (NEC) na jam'iyyar.
Shugaban BoT na PDP, Sanata Adolphus Wabara, ne ya yi sukar a wajen taron kwamitin a birnin tarayya Abuja a ranar Alhamis, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanata Adolphus Wabara ya bayyana cewa kwamitin zai ci gaba da ƙoƙarin kawo ƙarshen rikicin jam’iyyar ta hanyar yin taro da tsohon gwamnan jihar Rivers.
Za a yi zama da Nyesom Wike ne a watan Janairu, rahoton Vanguard ya tabbatar.
NEC: Kwamitin BoT na PDP ya damu
Sanata Adolpgus Wabara ya nuna damuwarsa kan yadda yawan ɗage taron NEC ya ci gaba da zubar da ƙimar PDP a wajen mambobinta.
"Dole ne na bayyana ɓacin ran wannan kwamitin kan yadda kwamitin NWC ke ci gaba da ɗage taron NEC."
"Mun yarda cewa ana iya samun ƙalubale wajen gudanar da harkokin mulki, amma mutunta lokaci abu ne wanda ba na wasa ba."
"A bisa haka, muna kira ga NWC da ya tabbatar lokacin da ya sanya na watan Fabrairun shekara mai zuwa, ya gudanar da taron NEC."
"Kwamitin BoT ba zai yi ƙasa a gwiwa ba wajen dawo da haɗin kai a cikin PDP. Bisa hakan za mu fara neman zaman lafiya a sabuwar shekara, inda za mu fara da Nyesom Wike, wanda muka yi alƙawarin sake ziyarta."
- Sanata Adolphus Wabara
Gwamnan PDP ya caccaki Ganduje
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde na jihar Oyo ya ja kunnen shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
Gwamna Makinde ya gargaɗi Ganduje da cewa ya shiga taitayinsa game da ikirarin da ya yi cewa APC za ta ƙwace jihohin Osun da Oyo a zaɓuka masu zuwa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng