"Za Mu Ba Ka Mamaki," Gwamna Ya Maida Martani ga Ganduje kan Ƙwace Jihohi 2

"Za Mu Ba Ka Mamaki," Gwamna Ya Maida Martani ga Ganduje kan Ƙwace Jihohi 2

  • Kalaman shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje na shirin kwace wasu jihohi sun fara shan raddi daga ƙusoshin jam'iyyar PDP
  • Gwamna Seyi Makinde ya ce Ganduje zai gamu da babban cikas kuma ba zai cimma nasara a zaɓukan da ke tafe a jihohin Oyo da Osun ba
  • Makinde ya yi ikirarin cewa ko nasarar da yake ganin APC ta samu a Edo da Ondo ba ta Allah da Annabi ba ce, za su tona abubuwan da suka yi a kotu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Osun - Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya gargaɗi shugaban APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje game da kalaman da ya yi bayan zaɓen Edo da Ondo.

Gwamna Makinde ya ja kunnen Ganduje da cewa ya shiga taitayinsa game da ikirarin da ya yi cewa APC za ta ƙwace jihohin Osun da Oyo a zaɓuka masu zuwa.

Kara karanta wannan

Ana shirin koyawa APC darasi, Ganduje zai fuskanci babbar matsala a wasu jihohi 2

Ganduje da Makinde.
Gwamna Makinde ya ce jihohin Osun da Oyo sun fi ƙarfin Ganduje da APC Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje, Seyi Makinde
Asali: Facebook

Seyi Makinde ya ce Ganduje ya yi gurgun lissafi kuma zai gamu da babban cikas a waɗannan jihohin guda biyu, kamar yadda Tribune Nigeria ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Seyi Makinde ya caccaki Ganduje

Makinde ya ce Oyo da Osun za su turnuke shugaban APC na ƙasa da barkono sannan za su ba shi mamakin da bai taɓa gani ba a rayuwarsa.

Gwamnan ya yi wannan martani ne a wurin kaddamar da wasu muhimman ayyukan tituna a Osogbo, babban birnin jihar Osun ranar Laraba.

A rahoton Punch, Makinde ya ce:

“Wani ya shagala bayan zaben jihohin Edo da Ondo, ya ce suna nan zuwa su karɓi Osun da jihar Oyo, ina rokonku da ku nuna musu barkono."
"Muna tabbatar masu cewa har yanzu wasan bai kare ba a Edo da Ondo, mun kai kara kotu saboda mu mutane ne masu bin doka da oda. Kuma mun yi imanin cewa duk abin da suka yi zai fito."

Kara karanta wannan

Gwamnan Legas ya yi magana kan kudirin harajin Tinubu, ya maida martani ga Zulum

Makinde ya jinjinawa takwaransa na Osun

Gwamnan Makinde ya nuna farin ciki da jin daɗi bisa ayyukan titunan da Gwamna Ademola Adeleke ke yi a jihar Osun.

Ya roƙi ɗaukacin al'ummar jihar Osun su sakawa Gwamna Adeleke bisa ayyukan alherin da yake masu ta hanyar sake zaɓarsa a karo na biyu.

An roki Oyetola ya sake tsayawa takara

A wani labarin, kun ji cewa yayin da ake tunkarar zaben gwamna a Osun, an fara rokon ministan Tinubu ya dawo ya sake neman takara a inuwar APC.

Wata kungiyar magoya bayan APC a Osun ta yi kira ga Adegboyega Oyetola ya ajiye kujerar minista, ya ceci jam'iyyar daga faɗawa cikin rigima.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262