'A Fassara Kudirin zuwa Harshen Hausa': 'Dan Majalisa a Arewa Ya ba da Shawara
- Yayin da ake cigaba da korafi kan kudirin haraji a Najeriya, dan Majalisar Tarayya ya yi korafi kan yan Arewa
- Dan Majalisar daga jihar Kogi, Hon. Abejide Leke ya ce mafi yawan masu korafin suna yi ne saboda siyasa da zaben 2027
- Hon. Leke ya shawarci fassara kudirin zuwa harshen Hausa duba da yadda matsalar ta fi yawa a Arewacin Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kogi - Dan Majalisar Tarayya daga jihar Kogi, Abejide Leke ya kare sabon kudirin haraji da Bola Tinubu ya kawo.
Dan Majalisar ya zargi masu korafi kan kudirin da makarkashiyar siyasa domin cimma burinsu a zaben 2027.
'Dan Majalisa ya ba da shawara kan batun haraji
Hon. Leke ya bayyana haka ne yayin hira da gidan talabijin na Channels a daren yau Laraba 4 ga watan Nuwambar 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Dan Majalisar ya ce wasu na amfani da addini domin kalubalantar wasu sassa na kudirin saboda cikar barinsu na siyasa cikin sauki.
Daga bisani, Leke ya ba da shawarar fassara kudirin zuwa harshen Hausa saboda an fi samun matsala daga Arewa.
Hon. Leke ya zargi wasu da siyasantar da kudirin
"Ina ba da shawarar a fassara wannan kudiri zuwa harshen Hausa saboda an fi samun matsala a Arewa idan aka kwatanta da Kudu."
"Na kadu duba da yawan mutane da suke korafi ba tare da karanta abin da ke cikin kudirin ba."
"Wannan ya tabbata cewa suna neman yadda za su kawo cikas ga Tinubu ne da siyasantar da lamarin saboda zaben 2027."
- Hon. Elder Abejide Leke
Malaman Musulunci sun magantu kan kudirin haraji
Mun kawo muku labarin cewa wasu malaman Musulunci a Arewacin Najeriya sun yi martani kan sabon kudirin haraji da ake ta ce-ce-ku-ce a kai.
Malaman da dama sun caccaki tsarin harajin inda suke korafin zai cutar da yankin Arewa da kuma kara jefa al'umma cikin mawuyacin hali.
Sai dai duk da haka wasu daga cikinsu sun bambanta kan kudirin, irinsu Sheikh Ahmad Mahmud Gumi sun nuna goyon bayansu ga kudirin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng