‘Yadda na Sha Fitsari a Gidan Yari’: Tsohon Hadimin Buhari Ya Tuna Mulkin Abacha

‘Yadda na Sha Fitsari a Gidan Yari’: Tsohon Hadimin Buhari Ya Tuna Mulkin Abacha

  • Tsohon hadimin Muhammadu Buhari a bangaren siyasa ya bayyana irin kalubalen da ya fuskanta a rayuwarsa
  • Tsohon sanatan jihar Ekiti, Babafemi Ojudu ya ce har fitsari ya sha a gidan yari domin ya rayu a zamanin sojoji
  • Sanata Ojudu ya kuma tuno yadda aka cafke shi sau fiye da 15 a zamanin mulkin marigayi Janar Sani Abacha

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ekiti - Tsohon sanata a Najeriya ya tuna baya inda ya bayyana irin wahalar da ya sha a zamanin mulkin Sani Abacha.

Sanata Babafemi Ojudu da ya wakilci Ekiti ta Tsakiya ya tuno yadda ya sha fitsari a gidan yari domin ya rayu.

Tsohon hadimin Buhari ya fadi yadda ya sha fitsari a gidan yari
Tsohon hadimin Buhari kuma sanata ya fadi yadda ya tsira da rayuwarsa a gidan kaso. Hoto: Ojudu Babafemi.
Asali: Facebook

Tsohon hadimin Buhari ya sha fitsari a gidan kaso

Sanata Ojudu ya bayyana haka ne yayin hira da yan jaridu a birnin Ado-Ekiti kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

"Ba talakawa ya kamata a tatsa haraji ba," Sanata Ibrahim ya kawo mafita

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ojudu wanda ya kasance tsohon hadimin Muhammadu Buhari a bangaren siyasa ya ce ya sha wahala a mulkin marigayi Sani Abacha.

A cikin wani littafi da ya wallafa kan rayuwarsa, Ojudu ya fadi yadda aka cafke shi har sau 15 daga 1993 zuwa 1997.

"Akwai lokacin da na sha fitsarina lokacin ina magagin mutuwa saboda babu maganin da aka ba ni kan fama da gudawa."
""Na taba karanta littafi da wani ke cewa shan fitsari yana da matsala, watakila na yi imani da fitsarin ne saboda ban ji komai ba bayan shan fitsarin."

- Babafemi Ojudu

Sanata Ojudu ya koka kan matsalolin Najeriya

Daga bisani Sanata Ojudu ya yi magana kan yadda za a shawo kan matsalolin Najeriya, cewar Daily Post.

Sanata Ojudu ya ce matsalolin kasar sun wuce maganar yin gyaran fuska a kundin tsarin mulkin kasar.

Gowon ya ceto ran Obasanjo a zamanin Abacha

A baya, kun ji cewa tsohon shugaban kasa, Janar Yakubu Gowon ya fadi yadda ya ceto rayuwar tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo.

Kara karanta wannan

'Yadda na roki Abacha afuwa domin ceto ran Obasanjo': Tsohon shugaban kasa ya magantu

Gowon ya ce ya roki marigayi Sani Abacha da ya yi afuwa ga Obasanjo kan zargin hannu a juyin mulki da aka yi a 1995.

Tsohon shugaban kasar ya ce ya rubuta takarda musamman ga Abacha, yake rokon ya yi masa afuwa kan zarginsa da ake yi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.