Peter Obi: Jam'iyyar LP ta Fara Shiri a Jihohi 36 domin Kawar da Tinubu a 2027

Peter Obi: Jam'iyyar LP ta Fara Shiri a Jihohi 36 domin Kawar da Tinubu a 2027

  • Jam’iyyar LP ta kaddamar da shirin sake tsara tsarin jagorancin jihohi da kuma shirin tunkarar zaɓen 2027
  • Jam’iyyar za ta kafa kwamitin jagoranci a jihohi domin ƙarfafa alaƙa tsakanin shugabanninta da kungiyoyin sa-kai
  • Shirin zai haɗa da horarwa da kuma shigar da sababbin mambobi cikin tsarin jam’iyyar a matakai daban-daban

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Jam’iyyar LP ta sanar da wani shirin gina tsarin jagoranci a jihohi 36 domin tunkarar zaɓen 2027 cikin ƙarfi da tsari.

Matakin ya biyo bayan ƙalubalen da jam’iyyar ta fuskanta a zaɓen 2023 tare da niyyar karfafa tsarin tafiyarta daga tushe.

Peter Obi
Jam'iyyar LP ta fito da shirin kafa shugabanci a jihohi. Hoto: Mr. Peter Obi
Asali: Facebook

Vanguard ta wallafa cewa LP za ta ƙaddamar da sabon tsarin shugabancin a hedkwatocin jam’iyyar a fadin Najeriya a ranar Juma’a.

Kara karanta wannan

An tarwatsa maboyar shugaban 'yan ta'adda, an kama gagararrun 'yan bindiga

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sake tsarin jam'iyyar LP a jihohin Najeriya

A sanarwar da jam’iyyar ta fitar, ta bayyana cewa za ta fitar da tsarin shugabanci mai kula da gangamin jama’a a matakin jihohi.

Haka zalika, sabon tsarin zai samar da shugabannin jihohi da ƙananan hukumomi tare da ba su horo na musamman da zai ƙarfafa su wajen gudanar da ayyukansu cikin nasara.

Yadda LP za ta kara samun 'yan jam'iyya

Tribune ta ruwaito cewa LP za ta tabbatar da cewa shugabannin gangami na jihohin da za a kaddamar sun samu horo tare da haɗa kai da ƙungiyoyi.

Bugu da ƙari, sabon tsarin zai ba wa mambobin ƙungiyoyi damar shiga jam’iyyar cikin sauƙi, inda za a tallafa musu wajen shiga sahun shugabanci ko zama wakilai a matakai daban-daban.

Yadda LP za ta tunkari zaben 2027

Jam’iyyar adawar ta bayyana cewa sabon tsarin ya tanadi kafa cibiyar jagoranci a jihohi da za ta haɗa shugabannin gangami, mataimakan su da wakilai.

Kara karanta wannan

Kudirin haraji: Kungiya ta shirya azumi domin Zulum da Ndume, ta fadi dalili

Ta kuma jaddada cewa jam’iyyar za ta zaɓi mambobi masu aminci da kishin jam’iyya, wadanda za su kasance masu haɗin kai da sahihiyar manufa wajen tunkarar zaɓen 2027.

An lallaba Jonathan ya yi takara a 2027

A wani rahoton, kun ji cewa an fara yunƙurin ganin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya sake neman shugabancin Najeriya a shekarar 2027.

Ƙungiyar Team New Nigeria ta fara sanya hotunan yaƙin neman zaɓen tsohon shugaban ƙasar a wasu wurare da ke birnin Kano.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng