Zaben 2027: Fastocin Goodluck Jonathan Sun Mamaye Birnin Kano
- An fara yunƙurin ganin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya sake neman shugabancin Najeriya a shekarar 2027
- Ƙungiyar Team New Nigeria ta fara sanya fastocin yaƙin neman zaɓen tsohon shugaban ƙasan a wasu wurare da ke birnin Kano
- Wannan dai ba shi ba ne karo na farko da ake buƙatar Jonathan ya sake neman shugabancin Najeriya bayan ya faɗi zaɓe a 2015
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Wata ƙungiya mai suna Team New Nigeria (TNN) ta fara yunƙurin ganin tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, ya tsaya takara a zaɓen 2027.
Ƙungiyar ta kafa fastocin yaƙin neman zaɓen Goodluck Jonathan a wasu wurare a jihar Kano, lamarin da ya sa aka fara raɗe-raɗi kan yiwuwar dawowarsa siyasa a 2027.
Fastocin Jonathan sun karaɗe Kano
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa an sanya fastocin ne a wurare irinsu babbar hanyar Gyadi-Gyadi/Zoo Road, Kofar Nasarawa da titin State Road.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Fastocin waɗanda ke da hotunan Jonathan, suna ɗauke da saƙon, "Team New Nigeria 2027: The Goodluck Nigeria Needs—Dr Goodluck Jonathan."
A kwanakin baya ne ƙungiyar TNN ƙarƙashin jagorancin Modibbo Yakubu Farakwai, ta ƙaddamar da kwamiti na jihar Kano domin ganin ta cimma manufarta.
Me Jonathan ya ce kan batun?
Sai dai, har yanzu ba a san ko Goodluck Jonathan ya amince da ayyukan ƙungiyar ba, na neman ya sake neman mulkin Najeriya.
Ƙoƙarin jin ta bakin mai magana da yawun bakinsa, Okechukwu Eze, ya ci tura.
TNN na son kawo canji a Najeriya
Da yake zantawa da manema labarai a Kano, Modibbo Yakubu Farakwai, ya ce ƙungiyar na ayyukanta ne sakamakon ƙaruwar buƙatar jama’a ta neman samun sabuwar alƙibla a siyasance.
"Ƴan Najeriya na son canji da kuma sha’awar kafa sabuwar jam’iyya mai sababbin fuskoki domin kawo canjin."
"Suna son a samu sauyi wajen tsari da yadda ake gudanar da mulki a kowane mataki."
- Modibbo Yakubu Farakwai
Jonathan ya gano matsalar Najeriya
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan ya bayyana cewa babbar matsalar da ke tunkarar Najeriya ta fuskar siyasa ita ce rashin haɗin kai.
Goodluck Jonathan ya ƙara da cewa ci gaba ba zai samu ga ƙasar nan ba, har sai an shawo kan matsalar.
Asali: Legit.ng