2023: Na Hannun Daman Buhari Ya Yi da Na Sanin Tallata Tinubu a Kano
- Jagora a jam'iyya mai mulki ta APC, AbdulMajeed Danbilki Kwamanda ya dauki zafi kan salon mulkin Bola Tinubu
- Ya bayyana takaicin yadda ake shan wahala a gwamnatin fiye da wacce aka sha a lokacin da Muhammadu Buhari ke mulki
- Danbilki Kwamanda ya bayyana nadama kan tallata Bola Tinubu a zaben 2023 da 'yan Najeriya su ka zabe shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Jigo a siyasar APC ta Kano, kuma masoyin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yi da na sanin zaben Bola Tinubu.
AbdulMajeed Danbilki Kwamandan ya ce sun tafka kuskure wajen tallata Tinubu, har ya samu nasarar zama shugaban Najeriya a inuwar APC.
A bidiyon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Danbilki Kwamnada ya bayyana takaicin mawuyacin halin da Arewacin Najeriya ta tsinci kanta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jigon APC ya fusata da 'gazawar' Tinubu
Wani mai amfani da shafin Facebook, Kwamred Nura Siniya ya wallafa bidiyon AbdulMajeed Danbilki Kwamanda ya na sukar salon mulkin Tinubu.
Dan Bilki Kwamanda ya ce;
"Yau babu tsaro, yau mutanen Zamfara amfanin gonarsu ya yi, amma su je su girbe babu. An kakkama mutane, da sauransu. Amfanin gonar baka isa ka girba ba. Akwai masifar da ta wuce wannan?
Fusataccen dan jam'iyyar ya kara da cewa;
"Mai Bola Tinubu zai ce mana? zaben da mu ka yi masa, ai gwara ma ba mu zabe shi ba. Domin duk masifar da mu ke ciki a gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari, mu na cikinta ai har ta fi na lokacin shugaba Muhammadu Buhari."
Kusa a APC na fatan karshen mulkin Tinubu
Jigo a APC da ke Kano, AbdulMajeed Danbilki Kwamanda ya bayyana rashin jin dadin yadda gwamnatin da jam'iyyarsa ke jagoranta ta gaza yi wa jama'a adalci.
"Amma wahalar da mu ke sha a karkashin gwamnatin Bola Tinubu, Allah Ka kawo mana mafita. Allah Ka kawo mana canji."
Dan takaran Kano ya gana da Peter Obi
A baya mun kawo labarin yadda tsohon dan takarar Sanata a Kano ta Tsakiya, AbdulSalam AbdulKareem Zaura ya yi ganawar sirri da tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi.
Obi ne ya ziyarci AA Zaura a gidansa da ke Abuja, inda manyan 'yan siyasar biyu su ka yabi kyawawan halayen juna, tare da nuna alamun su yi aiki tare yayin da zaben 2027 ke gabatowa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng