"Karshen Mulkin Tinubu Ya Kusa": Jigon PDP Ya Yi Hango Tasirin Ganawar Atiku da Obi
- Haduwar Atiku Abubakar da Peter Obi a Adamawa ya haifar da ce-ce-ku-ce kan ko 'yan adawar za su hada-kai gabanin 2027
- Jigon PDP, David Itopa ya ce akwai yiwuwar hadewar Atiku da Obi domin kalubalantar APC da kawo karshen Bola Tinubu
- Ana ganin rashin jituwar Atiku, Obi a 2023 ne ya jawo nasarar Bola Tinubu, amma an ce za su iya kai labari idan suka sake hada kai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Atiku Abubakar da Peter Obi sun sake jawo ce-ce-ku-ce a siyasar kasar nan bayan ganawarsu a gidan Atiku dake Adamawa.
Wannan ganawar ta kara rura wutar rade-radin cewa akwai yuwuwar 'yan adawar su kulla kawance a zaben 2027 mai zuwa.
Atiku Abubakar ne ya wallafa wani faifan bidiyo a shafinsa na X wanda ya nuna lokacin da yake karin kumallo tare da Peter Obi a gidansa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Illar rabuwar kan Atiku da Obi a 2023
Atiku da Obi sun kasance abokan siyasa a lokacin zaben shugaban kasa na 2019, inda Obi ya zama abokin takarar Wazirin a karkashin PDP.
To sai dai kuma sun yi hannun riga a shekarar 2023 lokacin da Obi ya yi takarar neman shugabancin kasar a karkashin jam'iyyar LP, wanda ya jawo APC ta samu nasara.
Masana harkokin siyasa na ganin cewa takara a jam'iyyu daban daban da Atiku da Obi suka yi ya share fagen samun nasarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Itopa: "Muna maraba da ganawarsu"
A kan hakan, David Itopa, jigo a jam'iyyar PDP, ya bayyana ra'ayinsa game da ganawar Atiku, Obi yayin wata tattaunawa da Legit.ng a ranar Asabar.
David Itopa, ya ce:
“Ziyarar da Obi ya kai wa Atiku a Adamawa ba sabon abu ba ne. Duka mutanen biyu na girmama juna.
"Duk da haka, a fagen siyasa, idan ana maganar hadewa tsakanin wadannan jiga-jigan 'yan siyasar, to abin maraba ne ne a garemu."
‘Karshen siyasar Tinubu ta kusa’ - Itopa
Itopa ya jaddada bukatar jam’iyyun adawa su hada karfi da karfe, inda ya bayyana yiwuwar kawancen Atiku da Obi a zai kawo sauyi ga yanayin siyasar Najeriya.
“Hanya daya tilo da za a iya kayar da jam’iyyar APC mai mulki karkashin Tinubu da kuma tsamo Najeriya daga kangin wahala ita ce jam’iyyun adawa su hada kai.
A cewar David Itopa, haɗin kai tsakanin jam'iyyun adawa tabbas zai kawo ƙarshen mulkin Tinubu.
Atiku ya fadi dalilin haduwarsa da Obi
A wani labarin, mun ruwaito cewa bangaren Atiku Abubakar da Peter Obi sun musanta labarin cewa sun gana a Adamawa ne domin kawance gabanin zaben 2027.
Hadimin Atiku a bangaren sadarwa, Paul Ibe shi ya ƙaryata labarin, ya ce haduwa ce ta tsofaffin abokai biyu kuma ba a tattauna wani batu na hadaka a ganawar ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng