Kudirin Sauya Fasalin Harajin Tinubu Ya Ƙara Gamuwa da Cikas a Jihar Kano
- Kudirin sauya fasalin harajin da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya gabatar a majalisar tarayya ya ƙara gamuwa da cikas a Kano
- Majalisar dokokin jihar Kano ta yi watsi da kudirin a zamanta na ranar Litinin, 2 ga watan Disamba, 2024
- Ta buƙaci sanatoci da ƴan majalisar wakilai musamman na Arewa su yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da kudirin bai tsallake ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Majalisar dokokin jihar Kano ta yi fatali da dokar sake fasalin haraji da ke gaban majalisar tarayya a halin yanzu.
Majalisar ta ɗauki wannan matsaya ne a zamanta na ranar Litinin, 2 ga watan Disamba, 2024 karkashin jagorancin kakakin majalisa, Rt. Hon. Ismail Falgore.
Leadership ta ruwaito cewa majalisar ta roƙi ƴan majalisar tarayya na Arewa su haɗa kai su kashe kudirin, kar su bari a zartar da shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kudirin haraji ya gamu da cikas a Kano
Shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin jihar Kano, Lawan Husseini (Dala, NNPP) ne ya gabatar da kudirin gaggawa kan batun sauya fasalin harajin Tinubu.
Lawan Husseini ya ce idan kudirin ya zama doka, babu inda za a maida kashin baya kamar Arewacin Najeriya.
Ya kuma bayyana cewa matakin da majalisar dattawa ta ɗauka na amincewa a yi wa kudirin karatu na biyu abin Allah wadai ne.
Yadda kudirin harajin zai yi wa Arewa illa
"Muna kallon kudirin a matsayin wani shiri da aka tsara da nufin zagon kasa ga tattalin arziki da ma kara wahalhalu da kuma talauta yankin Arewa gaba daya.
"Akwai damuwa a tsarin kasafta harajin VAT da ke kunshe a kudirin saboda wasu jihohin za su sha wahala wasu kuma kamar irinsu Legas za su samu kaso mai tsoka.
"Saboda manyan kamfanoni suna Legas, kaso 80 cikin 100 na harajin da aka tattara a Najeriya zai tafi ne zuwa jihar yayin da jihohin Arewa za su samu kaso ɗan kaɗan."
- Lawan Husseini.
Majalisar Kano ta ba ƴan majalisar Arewa shawara
Hon. Lawan Husseini ya ce hakan zai kara raunana wasu jihohin Arewa, yana mai bayyana cewa wasu daga cikinsu ba ma za su iya biyan albashi ba.
A ƙarshe, Majalisar dokokin Kano ta bukaci sanatoci da ƴan majalisar wakilai na Arewa su haɗa kai kuma su tabbata kudirin bai zama doka ba.
Tambuwal ya soki kudirin harajin Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya fito ya nuna adawarsa da ƙudirin haraji da Bola Tinubu ya ɓullo da shi.
Sanatan mai wakiltar Sokoto ta Kudu ya bayyana cewa sam ba yanzu ba ne lokacin da ya dace na fito da ƙudirin ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng