Awanni bayan Ziyartar Atiku, Peter Obi Ya Zauna da Jigon APC a Kano
- Tsohon dan takarar Sanata ta Tsakiya a Kano, AA Zaura ya fadi abin da ke burge shi game da Peter Obi na jam'iyyar LP
- Ya fadi haka ne bayan tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, ya kai ziyara ta musamman ga AA Zaura
- Daga bisani ne 'yan siyasar su ka shiga ganawar sirri, bayan sun yabi juna kan jajircewarsu wajen cigaba jama'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Tsohon dan takarar kujerar Sanatan Kano ta Tsakiya karkashin APC 2023, Abdulsalam Abdulkarim Zaura, wanda aka fi sani da AA Zaura, ya yabawa yadda Peter Obi ke neman hadin kai.
Yabon na zuwa ne kwana guda bayan Mista Obi ya ziyarci tsohon dan takarar shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar a gidansa da ke Adamawa.
Sakon da aka wallafa a shafin AA Zaura 'movement' 2023 a Facebook, ya ce tsohon dan takarar ya fadi haka ne a lokacin da Peter Obi ya kai masa ziyara gidansa da ke Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abubuwan da ke burge AA Zaura game da Obi
Jaridar This day ta ruwaito cewa tsohon dan takarar Sanata a Kano, AA Zaura ya ce yadda Peter Obi ya rike wuta wajen sharhi a kan al’amuran kasa, abin yabo ne.
Ya kara da cewa yadda tsohon dan takarar shugaban kasar ke son cigaban kasar nan, musamman wajen ganin ta tsaya da kafarsa na daga cikin abin da ke burge shi.
Takarar shugaban kasa: Zaura ya yabi Obi
AA Zaura ya jinjinawa Peter Obi kan yadda ya ke ta kokarin tattaro kan ‘yan siyasa a kokarinsa na sake neman kujerar shugaban Najeriya.
A nasa bangaren, Mista Obi ya yaba da tsayuwar da AA Zaura ke yi wajen ayyukan alheri, musamman ta karkashin gidauniyar AA Zaura Foundation.
Peter Obi ya hadu da Atiku
A wani labarin, mun ruwaito cewa hadimin tsohon dan takarar shugaban kasa a PDP, Paul Ibe ya yi karin haske kan dalilin haduwar Atiku Abubakar da takwaransa na LP, Peter Obi.
Mista Ibe, wanda shi ne hadimin tsohon mataimakin shugaban kasar a bangaren sadarwa, ya musanta cewa akwai wani shiri a kasa na hadaka tsakanin maigidansa da Mista Obi.
Asali: Legit.ng