"Babu Wanda Zai Canza Yin Allah," Gwamna Ya Faɗi Saƙon da Ake Turo Masa a Waya

"Babu Wanda Zai Canza Yin Allah," Gwamna Ya Faɗi Saƙon da Ake Turo Masa a Waya

  • Gwamna Biodun Oyebanji ya ce ba zai hana kansa barci saboda zaɓen gwamnan jihar Ekiti da ke tafe a 2026 ba
  • Oyebanji ya roki ƴan siyasa su daina turo masa sakonnin tes ta wayar tarho suna faɗa masa akwai matsala a kudirinsa na neman tazarce
  • Ƴa bayyana cewa babu wanda ya isa ya yi masa abin da Allah bai kaddaro ba, don haka ya buƙaci a kyale shi ya yi wa al'umma aiki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ekiti - Gwamnan Ekiti, Biodun Oyebanji ya nuna damuwa kan saƙonnin tes da wasu ƴan siyasa ke tura masa suna nuna masa akwai matsala a shirinsa na tazarce.

Gwamna Oyebanji ya bayyana cewa ba zai hana idonsa barci ba saboda kawai yana neman al'ummar Ekiti su sake zaɓensa a karo na biyu a 2026.

Kara karanta wannan

Matasan Arewa sun yi magana kan goyon bayan Shugaba Tinubu a zaɓen 2027

Gwamna Oyebanji.
Gwamna Oyebanji ya ce ba zai hana kansa barci saboda zaben Ekiti na 2026 Hoto: Dr. Biodun Oyebanji
Asali: Twitter

Gwamna ya faɗi saƙon da ake turo masa

Ya ce ko a jikinsa bai damu da matsalar da ƴan siyasa suka hango masa ba a zaɓen gwamnan jihar Ekiti da za a yi a 2026, kamar yadda Punch ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Oyabanji ya buƙaci ‘yan siyasa su daina aika masa irin wadannan sakonnin ta wayar tarho domin hankalinsa na kan shugabanci da cika alƙawurran da ya ɗauka.

Gwamnan ya yi wannan jawabi ne a Ado Ekiti a daren Juma’a a wajen taron Yabo da Ibada na wata-wata a dakin taro na Jibowu da ke gidan gwamnatin Ekiti.

"Mulki na Allah ne - Gwamna Oyebanji

"Na yi imani da cewa tsarin Allah ya zarce tunanin duk wani ɗan adam, ba zan hana kaina barci ba, komai yana hannun Allah.
."Duk abin da Allah bai kaddaro wa bawansa ba, ba zai taɓa samun shi ba kuma idan Allah ya yanke hukunci babu mai ja da shi.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kaduna ya ba ƴan bindiga kuɗi domin su tuba? Gaskiya ta bayyana

"Ina faɗa maku wannan ne saboda ku daina turo mani saƙonni kuna gaya mun akwai damuwa a zaɓen da muke tunkara a 2026, ku bar komai a hannun Allah."

- Biodun Oyebanji.

Matasan Arewa sun magantu kan tazarcen Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa matasan Arewa sun bayyana cewa har yanzun ba a kai ga cimma matsaya kan marawa Tinubu baya ya yi tazarce ko akasin haka ba a 2027.

Shugaban ƙungiyar matasan (AYCF), Yerima Shettima ya ce duk wanda ya ce Arewa ta ɗauri ɗamarar yaƙar Bola Tinubu ƙarya yake.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262